Mai Safarar Makami ga 'Yan Bindiga da Ya Nemi Taimakon Soja Ya Shiga Hannu

Mai Safarar Makami ga 'Yan Bindiga da Ya Nemi Taimakon Soja Ya Shiga Hannu

  • An kama wani matashi a Abuja bisa zargin shirin sayen harsashi domin ba ’yan bindiga da ke addabar Zamfara,
  • Rahotanni sun nuna cewa matashin da aka kama ya nemi taimakon wani soja yana neman ya sama masa harsashi har 1,000
  • ’Yan sanda sun ce ana bincike domin gano sauran masu hannu a lamarin bayan gano wani adadi na kuɗi a hannunsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Rundunar ’yan sandan Abuja ta kama wani mutum mai shekaru 32, Ahmed Abubakar, bisa zargin shirin sayen harsashi domin ’ba yan bindiga da ke kai hare-hare a jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce an kama matashin ne a ranar 7, Disamba, 2025 bayan jami'an tsaro sun samu bayanan sirri game da shi.

Kara karanta wannan

Tsaro: Malaman Musulunci, Kirista sun fadawa Tinubu gaskiya, sun hango barazana

Sufeton 'yan sandan Najeriya.
Shugaban 'yan sandan Najeriya yana bayani a ofis. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa Abubakar dan asalin Gusau da ke zama a Gwagwalada ya nemi taimakon wani soja mai suna Kofur Yusuf Mohammed domin samo masa harsashi har guda 1,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama mai safarar makamai a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar ya shiga hannun jami’an Mabushi ne bayan da suka samu sahihin bayani game da aikinsa.

A cewar bayanan da Punch ta wallafa, an kama shi ne da misalin ƙarfe 3:30 na yamma yayin da ake bibiyar shirin da ake zargin yana yi.

An ce Abubakar ya nemi soja ya samo masa harsashi domin ba ’yan bindiga a Zamfara, inda ya ce zai ba shi lada mai yawa.

Ana cigaba da bincike kan lamarin

Bayan tsanata bincike, an ce Abubakar ya amsa cewa yana aiki ne karkashin umarnin kawunsa, Ahmed Yakubu, wanda yake zama a gidan da suke amma yanzu ya tsere.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ganduje ya fara raba fom din shiga aikin sabuwar Hisbah a Kano

Yakubu ne, a cewar shi, ya umarce shi ya saye harsashin sannan ya kai su Zamfara domin ba ’yan bindigar da ke yankinsu.

Kakakin 'yan sandan Abuja
Mai magana da yawun 'yan sandan Abuja, Josephine Adeh. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Jami’an tsaro sun gano N170,100 a wurinsa, wanda ake zargin wani ɓangare ne na kuɗin da aka ware don cinikin da ake shirin yi.

’Yan sanda sun ce Abubakar yana hannunsu yanzu, kuma ana ci gaba da bincike domin gano duk wanda yake da hannu a wannan lamari.

'Yan sanda ba su amsa waya ba

Kakakin rundunar ’yan sandan FCT, Josephine Adeh, ba ta amsa kiran wayar ’yan jarida ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Haka kuma bata yi martani ba game da saƙon da aka tura mata, abin da yasa ake tunanin lamarin yana cikin wani mataki na tsaro da ba a son sakin bayanai baki daya.

An kama mai garkuwa da mutane a Ondo

A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta kama wani da ake zargi da garkuwa da mutane.

Bayanin da 'yan sanda suka fitar ya nuna cewa an cafke mutumin ne a lokacin da ya ke kokarin cire kudi ta POS.

Kara karanta wannan

'Ku daina sayen motocin alfarma,' Muhimmin sakon Dangote ga masu kudi a Najeriya

An ce mutumin ya shiga gidan wata mata ne a Ondo da bindiga ya bukaci ta bayar da kudin fansa har Naira miliyan 1.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng