Manyan Sarakunan da Aka Nada a Arewacin Najeriya a Shekarar 2025
Masarautun gargajiya na da dadadden tarihi a yankin Arewacin Najeriya, inda ake daukarsu da matukar muhimmanci.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Wadannan masarautun da ke da dadadden tarihi suna da sarakuna wadanda ke jagorantar harkokin mulkin gargajiya.

Source: Facebook
Manyan sarakunan Arewa da aka nada a 2025
Legit Hausa ta yi duba kan manyan sarakunan da suka hau karagar mulki a Arewacin Najeriya a shekarar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yawa daga cikin sarakunan dai sun hau kan karagar sarauta ne bayan rasuwar wadanda suka gabace su.
1. Sarkin Gusau
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya naɗa Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau a ranar, 30 ga watan Yulin 2025, cewar rahoton jaridar The Punch.

Source: Facebook
Ya hau gadon sarauta ne a matsayin Sarki na 16, bayan rasuwar mahaifinsa, Ibrahim Bello, wanda ya yi mulki na tsawon shekara 10 kafin ya rasu a ranar 25 ga watan Yuli, 2025.
Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Abubakar Nakwada, ya ce an naɗa shi ne bisa tsarin masarautar gargajiya da shawarar masu zaben sarki.
Kafin samun sarautar sarki, shi ne yake rike da sarautar Bunun Gusau.
Gwamna Dauda Lawal, yayin taya sabon sarkin murna, ya umarce shi da ya tsaya kan kyakkyawan tarihin da kakanninsa suka bari, musamman ganin cewa ya fito daga zuriyar Malam Sambo Dan Ashafa.
Ya kuma bukaci sabon sarkin ya zama jagoran kawo hadin kai, zaman lafiya da cigaba, tare da inganta zaman tare cikin lumana a Masarautar Gusau da ma wajen ta.
2. Sarkin Gudi
A ranar, 3 ga watan Agustan 2025, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da naɗin Hon. Ismaila Ahmed Gadaka a matsayin sabon Mai Gudi, bayan rasuwar tsohon sarkin, Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Kaji.
Hon. Ismaila Ahmed Gadaka ya kasance ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Fika/Fune (2011–2019), kuma ya taba zama kwamishina a jihar Yobe (2007–2010), rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.
Kafin naɗinsa, yana rike da sarautar Yariman Gudi, alamar dangantakarsa da al’adun masarautar.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Amurka mai sukan Najeriya kan tsaro ya sassauto, ya yaba wa Tinubu
Gwamna Mai Mala Buni, yayin amincewa da naɗin, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa sabon sarkin zai kare darajar masarautar tare da bayar da gudunmawa ga ci gaba, zaman lafiya da haɗin kan jihar Yobe.
3. Sarkin Zuru
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da naɗin Sanusi Mika’ilu Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru a ranar, 28 ga watan Agustan 2025, tashar Channels tv ta kawo rahoton.
An naɗa shi ne bayan rasuwar tsohon sarki, Muhammad Sani Sami Gomo II, wanda ya rasu a ranar 16 ga Agusta, 2025 a asibiti da ke birnin Landan.

Source: Facebook
Gwamna Nasir Idris ya amince da nadin ne cikin wata takarda da kwamishinan harkokin masarautu, Garba Umar Dutsin-Mari ya gabatar a masarautar Zuru.
Garba Umar Dutsin-Mari ya ce daga cikin ’yan takara uku da aka tantance, Alhaji Sanusi Mika’ilu Sami ne ya samu mafi yawan kuri’u, wanda hakan ya sa aka zaɓe shi domin ya hau kan sarauta.
Kwamishinan ya gode wa gwamnan bisa gaggauta amincewa da naɗin, tare da shawartar sabon sarkin da ya tabbatar da ya yi jagoranci bisa gaskiya da adalci.
Jaridar Daily Trust ta ce Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa ya naɗa shi ne saboda kasancewarsa zabin jama’a.
“Ni ban san shi ba a baya, amma na umarci a gudanar da cikakken bincike kan wanda mutane suka fi so, kuma dukkansu suka ambaci sunan Sanusi. Nan da nan na amince da naɗinsa."
- Gwamna Nasir Idris
4. Sarkin Duguri
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da naɗin Adamu Mohammed, babban ɗan uwansa, a matsayin sabon Sarkin Duguri, a karamar hukumar Alkaleri.
Kafin naɗinsa, Adamu Mohammed ya kasance yana shugabantar hukumar kula da ilmi ta BASUBEB a jihar Bauchi.
Sakataren gwamnatin Bauchi, Aminu Hammayo, yayin miƙa takardar naɗi, ya ce an zabe shi saboda kyakkyawan tarihin aikinsa da gudummuwarsa ga cigaban jihar.
Aminu Hammayo ya yi wa sabon sarkin nasiha da ya ja ragamar masarautar da gaskiya, tsoron Allah, tare da tallafawa manufofin gwamnati domin inganta rayuwar jama’a.
An nada sabon Olubadan na Ibadan
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Rashidi Adewolu Ladoja, ya zama sabon Olubadan na Ibadan.
An tabbatar da nadin sabon Sarkin a hukumance ne a bikin da aka gudanar a jihar Oyo da ke Kudancin Najeriya a ranar, 26 ga watan Satumban 2025.
Gwamna Seyi Makinde ya mika sandar mulki ga sabon Sarkin Ibadan, Oba Ladoja, wanda ya kara tabbatar da nadinsa a matsayin Olubadan na 44.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


