Jama'a Sun Fito Titunan Sakkwato Murnar Hallaka Kasurgumin Ɗan Ta'adda

Jama'a Sun Fito Titunan Sakkwato Murnar Hallaka Kasurgumin Ɗan Ta'adda

  • Dakarun Sojojin Najeriya sun fitar bayanai a kan yadda ta hallaka babban jagoran ‘yan ta’adda, Kalamu, a Sakkwato
  • Al’ummar Sabon Birni sun fito suna murna bayan shafe shekaru suna fuskantar garkuwa da mutane da hare-hare da Kalamu ya jagoranta
  • Sojoji sun fatattaki maharan, sun hallaka 11, sun kuma kwace bindigu, alburusai masu yawa da illata miyagun mutanen da dama

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sakkwato – Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar cewa fitaccen shugaban ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Kalamu ya baƙunci barzahu.

Kalamu da ya fitini mazauna Sakkwato da kewaye na daga cikin ‘yan ta’addan da Dakarun musamman na unduna ta takwas suka hallaka a wani samame da suka kai jihar.

Kara karanta wannan

Tsaro: Malaman Musulunci, Kirista sun fadawa Tinubu gaskiya, sun hango barazana

Sojoji sun yi ragargaza yan ta'adda
Wasu daga cikin sojojin Najeriya Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa an tabbatar da hakan bayan dogon bincike da tabbatar da sahihan bayanan sirri game da mutuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun hallaka ɗan ta'adda

Jaridar Punch ta wallafa cewa Kalamu ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu haddasa tarzoma a yankin Sabon Birni, inda ya dade yana jagorantar hare-hare, garkuwa da mutane.

Baya ga harin zalunci da ya rika jagoranta, Kalamu na kai harin daukar fansa daga talakawa bayan dakaru sun farmaki tawagarsa.

Mutuwarsa ta jefa mazauna kauyuka da dama da suka sha fama da azabarsa a cikin farin ciki, inda suka fito nuna jin dadinsu.

Al’umma sun yi murna da kashe ɗan ta'adda

Bayan kammala aikin, mazauna kauyuka da dama a Karamar Hukumar Sabon Birni sun fito kan tituna suna murnar nasarar sojojin a kan yan ta'adda.

Mutanen yankin sun bayyana cewa sun ɗauki dogon lokaci suna fuskantar zalunci da tsangwama daga ‘yan bindigan da Kalamu ke jagoranta

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi bayani game da jirgi da sojinta da ke tsare a Kasar Burkina Faso

Dakarun runduna ta takwas sun dakile yunkurin wasu ‘yan ta’adda masu dauke da makamai da nufin kutsa wani kauye a Sakkwato.

Rahotanni sun ce sojojin sun yi artabu mai zafi da maharan, wanda ya kai ga hallaka 11 daga cikinsu, sannan akwai alamun jini da ke nuna cewa sauran sun gudu da raunuka.

An kashe yan ta'addan da dama a Sakkwato
Taswirar jihar Sakkwato da ke fama da ƴan ta'adda Hoto: Legit.ng
Source: Original

Majiyar soja ta ce:

“Da safiyar 8 ga Disamba, 2025, Rundunar Musamman ta takwas ta mamaye maboyar ‘yan bindiga a Kurawa, Sabon Birni. Yan ta’addan suna kokarin kai farmaki Tara village, amma an dakile su.”

Sojojin sun kwace bindigun AK-47 guda takwas, mujallu guda biyar, da harsasai 26.

Ƴan ta'adda sun hallaka bayin Allah

A baya, mun ruwaito cewa Shugaban karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato, Alhaji Ayuba Hashimu, ya karyata rahotannin cewa ’yan bindiga sun kai hari yankinsa.

Wasu rahotanni da suka fara yawo a shafukan sada zumunta na cewa an kai hari wani masallaci tare da kashe Liman da wasu masallata a yayin da suke ibada.

Alhaji Ayuba Hashimu bayyana cewa babu wani abu makamancin haka da ya faru a yankin, ya ce labarin ya fito ne daga majiya mata tushe ko makama.

Kara karanta wannan

Malami, Buratai, Emefiele da wadanda aka yi zargi suna daukar nauyin ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng