'Za a Iya Kara Fuskantar Juyin Mulki a Afirka ta Yamma,' Femi Falana
- Babban lauya, Femi Falana ya ce Najeriya ba za ta jagoranci yaki da juyin mulki ba sai ta magance matsalolin cikin gida
- Ya gargadi gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta daina fada da damar fadin albarkacin baki da matsa wa 'yan adawa
- Lauyan ya yi kira ga hukumar zabe ta kasa INEC ta bude kofa domin jam’iyyun da ke da akidar siyasa su samu damar rajista
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sanannen lauya kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya ce Najeriya za ta gaza shawo kan juyin mulki a yammacin Afirka muddin ta ki magance matsalolin cikin gida.
Lauyan ya yi wannan bayanin ne lokacin da kasashen Yammacin Afrika ke sake fuskantar kalubalen juyin mulki.

Source: Twitter
Falana ya bayyana matsayarsa ne a shirin Politics Today na Channels Television, inda ya jaddada cewa matsalolin tattalin arziki, talauci, jahilci da rashin tsaro suna daga cikin manyan abubuwan da ke sa jama’a tawaye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce idan ana son ingantacciyar dimokuradiyya, dole gwamnati ta bude sarari ga ’yancin fadin albarkacin baki, ta kare ’yancin dan kasa, kuma ta daina daukar suka a matsayin laifi.
Yadda Najeriya za ta hana juyin mulki
Falana ya ce ba zai yiwu Najeriya ta jagoranci kokarin hana juyin mulki a yammacin Afirka ba alhali tana da matsaloli da dama a cikin gida da ke da tasiri kai tsaye ga zaman lafiya.
Ya ce dole ne a gyara tattalin arziki, a rage talauci, a yaki jahilci, sannan a tabbata an kare rayuka da dukiyoyin al’umma domin a samu daidaito.
Ya kara da cewa dimokuradiyya ba za ta zauna kafafunta ba idan ana takura ’yancin fadin albarkacin baki, musamman ta hanyar gurfanar da mutane bisa laifuffuka iri-iri saboda su kawai sun yi magana kan al’amuran kasa.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta dauki matakai 3 bayan sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Benin
Falana ya ce idan har Najeriya na son ta dakile juyin mulki a yankin, dole ta fara gyara gidanta, ta tabbatar da dimokuradiyya ta samu karfi, sannan ta kare 'yan adawa domin a samu cikakkiyar siyasa mai tasiri.
Barazanar karin juyin mulki a Afrika
Falana ya ce ba abin mamaki ba ne idan karin juyin mulki suka faru a yammacin Afirka, domin yanayin siyasa da takura da dimokuradiyya ke fuskanta na kara zurfafa fushi a zukatan jama’a.
Ya ambaci misalin kasar Benin, inda yunkurin juyin mulki ya faru bayan wasu sojoji karkashin Laftanar Kanal. Pascal Tigri suka mamaye gidan talabijin a Cotonou.
Falana ya yi gargadin cewa kasashen Afirka, musamman Najeriya, ba su da cikakkiyar dimokuradiyya lura da ana ci gaba da takura 'yan adawa ko kuma ana korar shugabannin adawa zuwa gudun hijira.
Punch ta rahoto ya ce irin wannan yanayi yana haifar da juyin mulki, domin mafi yawan sojojin da ke yin bore suna dogara ne ga korafe-korafen da ake yi.
Falana ya nemi INEC ta yi rajistar jam'iyyu
A cewar Falana, akwai bukatar hukumar zabe ta INEC ta fadada damar shiga siyasa, ta hanyar barin jam’iyyun da ke da akida su samu rajista domin kalubalantar tsarin da ake ciki.
Ya ce matsin siyasa da rashin yarda da adawa na daga cikin abubuwan da ke haifar da rashin jituwa da rashin kwanciyar hankali a nahiyar.

Source: UGC
Faransa ta hana juyin mulki a Benin
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin kasar Faransa ta fadi rawar da ta taka wajen hana yunkurin juyin mulki nasara a Benin.
Wani hadimin shugaba Emmanuel Macron ya ce sun taimaka da bayanan leken asiri da suka hana sojojin kasar nasara.
Sai dai duk da haka, Faransa ba ta fitar da bayanai dalla-dalla game da rawar da ta taka yayin da ta kai agaji kasar Benin ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
