Abin da Buratai Ya Ce ga Tinubu bayan Kokarin Dakile Juyin Mulki a Benin
- Tsohon hafsan sojoji a Najeriya, Tukur Buratai ya yi magana irin ta sojoji bayan yunkurin juyin mulki a Benin
- Buratai ya kira sunan Shugaba Tinubu na musamman a cikin bayanansa game darawar da ya taka
- Tsohon sojan ya gargadi cewa juyin mulki a Benin zai haifar da barazana ga iyakar Najeriya da ƙara yawaitar miyagun hanyoyi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon hafsan sojojin Najeriya, Laftanar-Janar Tukur Buratai mai ritaya ya tsoma baki kan halin da ake ciki a Benin.
Buratai wanda yanzu Jakada ne a Jamhuriyar Benin, ya jinjinawa Shugaba Bola Tinubu bisa umarnin da ya bayar na gaggauta tura sojoji.

Source: Twitter
Benin: Kalaman Buratai game da kokarin Tinubu
Buratai ya bayyana haka a Abuja ranar Talata 9 ga watan Disambar 2025, inda ya yabawa Bola Tinubu kan daukar mataki, cewar Zagazola Makama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce tura jiragen yaƙin saman Najeriya da dakarun ƙasa bisa buƙatar gwamnatin Benin ya nuna “ hangen nesa, ƙarfin siyasa da ingantaccen tsari na soja.”
Tsohon sojan ya ce an yi hakan ne domin murkushe yunƙurin juyin mulki a ƙasar, yana kiran matakin a matsayin “dabara” da ta kare dimokuradiyya tare da hana rikicin yankin ya faɗaɗa.
Ya ce masu suka suna kwatanta lamarin da matsalolin tsaron cikin gida ba su fahimci bambancin barazanar ba.
A cewarsa, aikin da aka gudanar a Benin ya kasance babban farmakin soja na gargajiya da ya nufa wuraren da sojojin tawaye suka mamaye, nau’in aikin da rundunar ƙasa ke da cikakkiyar bajinta a kai.
Ya ce irin wannan farmaki na amfani da karfi, rinjayen iska da dakarun ƙasa masu horo ya ba Najeriya nasara cikin gaggawa.

Source: Twitter
Illar da rikicin Benin zai kawo Najeriya
Buratai ya jaddada cewa wannan nasarar ba za a kwatanta ta da yaƙin cikin gida ba, domin rikicin Nigeria na gida ya shafi ‘yan ta’adda masu amfani da bayanan leƙen asiri da dabarun ɓoyayyun hare-hare.
Ya ce nasara a irin wannan yaƙi tana buƙatar haɗin kai na leƙen asiri, ‘yan sanda, cigaban tattalin arziki da shirye-shiryen jin ƙai.
Ya ce yabo ga Tinubu kan abin da ya yi a Benin bai nufi suka ga yadda ake magance matsalolin cikin gida ba, illa dai gane cewa dabaru daban ake amfani da su a yaƙe-yaƙe daban.
Buratai ya kuma jaddada muhimmancin siyasar yankin, yana cewa nasarar juyin mulki a Benin za ta iya haifar da babbar barazana ga yammacin Najeriya.
Ya ce:
“Idan Benin ta rikice, manyan hanyoyi za su buɗe ga ‘yan ta’adda, za a samu kwararar ‘yan gudun hijira, sannan barazanar iyaka za ta ninka."
Buratai ya musanta alaka da ta'addanci
An ji cewa tsohon hafsan sojojin kasa a Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya magantu bayan saka sunansa cikin zargin taimakon ta'addanci.
Buratai ya yi karin haske ne kan zargin da ke cewa yana da hannun kai tsaye ko kaikaice wajen daukar nauyin ta’addanci.
Akwai mutane da dama ciki har da tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari da ake zarginsu da wannan mummunan laifi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

