Daura Za Ta Yi Cikar Fari: Za a Naɗa Rarara Sarautar 'Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa'

Daura Za Ta Yi Cikar Fari: Za a Naɗa Rarara Sarautar 'Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa'

  • Mai martaba sarkin Daura, Faruk Umar Faruk zai naɗa fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara sarautar Sarkin Wakar Kasar Hausa
  • Rarara ya gayyaci jama’a zuwa nadin sarautar da za a yi masa a ranar Asabar, wacce za ta ƙara ɗaga matsayin wakokinsa a kasar Hausa
  • Sai dai, wasu masoya tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, sun ce bai kamata masarautar Daura ta yi wa Rarara nadin sarauta ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Masarautar Daura za ta yi cikar fari a karshen makon nan yayin da aka shirya yin nadin sarautar 'Sarkin Wakar Kasar Hausa'.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk ne zai naɗa fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, wannan sarauta.

Za a yi wa Dauda Kahutu Rarara nadin sarautar Sarkin Wakar Kasar Hausa a Daura
Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya yi shirin nadin sarautar da za a yi masa a Daura. Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Source: Facebook

Za a yi wa Rarara nadin sarauta a Daura

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya gaji da rikicin PDP, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Mawaki Dauda Kahutu Rarara da kansa ne ya sanar da lokacin nadin sarautar a wani sakon goron gayyata da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sakon da ya wallafa a daren ranar Talata, 9 ga Disamba, 2025, Rarara ya bai dauke wa duk mai dama zuwa wannan bikin nadin sarauta ba.

Mawaki Rarara ya wallafa cewa:

"Ina gayyatar kowa da kowa zuwa wajen nadin sarautata, mai taken 'Sarkin Wakar Kasar Hausa,' sarautar da mai alfarma sarkin Daura yayi min.
"Za’ayi nadin a fadar mai martaba sarkin Daura a ranar Asabar, 13 ga Disamba, 2025, Insha Allah."

An soki sarkin Daura kan sarautar Rarara

Tun kafin a sanya ranar da za a yi wa Rarara nadin sarautar Sarkin Wakar Hausa, Legit Hausa ta rahoto cewa wasu sun dauki zafi kan wannan nadi.

Wani masoyin tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari, mai suna Abdullahi Haruna Izge, ya bayyana mamaki da fushi a kan yadda masarautar Daura ta nada Rarara sarauta.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, mai taken 'Mu masoya Buhari, mun ji an ci amanarmu,' Abdullahi Izge ya ce wannan mataki na masarautar cin amana ne ga magoya bayan Buhari.

Kara karanta wannan

Bidiyo: 'Yan bindiga sun kashe matar malamin addini, sun kona masa gida da mota

Abdullahi Haruna Izge ya ce bai dace masarautar Daura ta dauki irin wannan mataki ba tare da la'akari da yadda Rarara ke nuna rashin da'a ga Buhari.

"Mu a matsayina na masoya Buhari, mun ji an ci amana ƙwarai bayan masarautar Daura ta ba wa Rarara sarauta, a masarautar da tsohon Shugaba Buhari ya dauka da kima da daraja, kuma ya ke karbar shawarwari.”

- Abdullahi Haruna Izge.

Masoyan Buhari sun caccaki masarautar Daura kan yi wa Rarara sarautar Sarkin Wakar Hausa.
Dauda Kahutu Rarara na cikin farin ciki lokacin da wata jami'a ta ba shi kambun 'Dakta'. Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Source: Facebook

An yi ce-ceku-ce kan sarautar Rarara

Sai dai, a hannu daya, dubunnan masoyan fitaccen mawakin, sun yi dafifi a shafinsa na Facebook, inda suka taya shi murnar samun wannan sarauta, yayin da wasu suka kushe hakan:

Shehu Isyaku Sulaiman:

"Naziru ne sarkin Waka"

Sulaiman Abubakar Bolari:

"Da fatan zakayi amfani da wannan damar ka nemi afuwar marigayi Shugaba Buhari da iyalansa da kuma miliyoyin magoya bayansa bisa ga munanan kalaman da kayi a kansa lokacin da ya sauka daga kan mulki."

Abba Sha Iri:

"Allah ya kara basira ciyaman."

Bilal Aminu:

"Sarkin mashirmatan kasar Hausa dai."

Bashiru Ahmad:

"AlhamdilLah Allah S.W.T yasa alkairi, ya sa hakan ya zamo cigaban yankinmu na Arewa gaba daya amin. Allah ya cigaba da dafama ka zarce inda makiyanka basa so suga kaje."

Kara karanta wannan

Tsohon kakakin PDP na kasa ya bi sahun gwamnoni 5, ya fice daga jam'iyyar

Alhaji Abba Kyari:

"Dr. ya zama sarki."

'Dalilin ba ni kambun Dakta' - Rarara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’ar European American ta ba fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara lambar yabo ta 'Dakta' saboda shahararsa a waka.

Rarara ya fito ya musanta zargin cewa biyan kudi ya yi don samun digirin, inda ya ce karamawar ta biyo bayan gudunmawarsa ga al’umma, yaren Hausa da siyasa.

A cewarsa, jami’ar European American ta yaba masa ne saboda kokarinsa wajen kula da jama’a da rawar da ya taka a siyasa da bunkasa harshen Hausa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com