Bayan sukar shugaba Buhari a waƙa, Fitaccen Mawakin Siyasa, Dauda Rarara, ya magantu kan manufarsu

Bayan sukar shugaba Buhari a waƙa, Fitaccen Mawakin Siyasa, Dauda Rarara, ya magantu kan manufarsu

  • Shahararren mawakin shugaban ƙasa Buhari, Dauda Adamu Rarara ya zayyana manufarsu ta kungiyar 13-13 da yan Kannywood suka kafa
  • Rarara ya ce kungiyar ba ta da alaƙa da siyasa amma a shirye take ta yi aiki da jam'iyyun siyasa wajen kawo cigaba a Kannywood da ƙasa
  • Ya ce an kafa 13-13 ne da nufin tafiyar da masana'antar Hausa a zamanance da kuma tallafa wa masu ƙaramin karfi

Kano - Fitaccen mawaƙin siyasar nan masoyin Buhari, Dauda Adamu Rarara, ya bayyana wa al'umma maƙasudin kafa kungiyar 13-13 wacce ta haɗa mawaƙan Kannywood da Jaruman Fim a sassan ƙasar nan.

Daily Trust ta rahoto cewa Rarara ya yi jawabi ne yayin raba dumbin tallafin kayan abinci da kuɗaɗe da ƙungiyar ta samu daga shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Deborah: Kungiyoyin Musulmai 13 sun aike da sako ga Gwamnatin Buhari game da Zagin Annabi SAW

Dauda Adamu Rarara.
Bayan sukar shugaba Buhari a waƙa, Fitaccen Mawakin Siyasa, Dauda Rarara, ya magantu kan manufarsu Hoto: @real_dauda_kahutu
Asali: Instagram

Rarara ya ce ƙungiyar ba ta siyasa bace kuma ba don siyasa aka kafa ta ba, amma a cewarsa ɗaya daga cikin makasudin kafa ta shi ne ta kara ɗaga darajar masana'antar Hausa.

Mawaƙin, wanda kwanakin baya ya yi wakar da ta shafi tsaro karƙashin 13-13, ya ce babbar manufar da suka sa a gaba shi ne ƙara danƙon haɗin kai a masana'antar da kuma ayyukan jin ƙai ga ƙasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rarara ya ƙara da cewa ƙasancewar 13-13 ba ƙungiyar siyasa bace, za su yi aiki da duk wata tafiyar siyasa da ta shirya tallafawa wajen cigaban masana'antar Kannywood da kuma ƙasa baki ɗaya.

Shahararren mawakin dai shi ne shugaban kungiyar wacce suke wa laƙabi da 13-13, kuma ƙungiyar na da mambobi a mafi yawan jihohin Arewacin Najeriya.

Zauwa yanzu dai kungiyar ta ja hankalin ɓangaren nishaɗantarwa musamman a arewacin Najeriya yayin da suke ayyukan taimako da jin kai a ɓangarori da dama na kyautatawa ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma da hadiminsa a mahaifar gwamnan Arewa

A wani labarin kuma Fusatattun Mutane sun yi ajalin wani dan fashi da dubunsa ta cika a jahar Katsina

Mutane sun yi ajalin mutum ɗaya daga cikin tawagar yan fashi da dubunsu ta cika a karamar hukumar Charanchi ta jihar Katsina.

Bayanai sun nuna cewa yan sanda sun kai ɗauki dan kama yan fashin bayan sun kwace motar wani Abdulmumini a gona.

Asali: Legit.ng

Online view pixel