'Dalilin da Ya Sa Juyin Mulki ba Zai Taɓa Yiwuwa a Najeriya ba'

'Dalilin da Ya Sa Juyin Mulki ba Zai Taɓa Yiwuwa a Najeriya ba'

  • Tsohon soja a Najeriya, Janar John Enenche mai ritaya ya yi magana kan yiwuwar juyin mulki a kasar da ke makwabtaka da Benin
  • Enenche ya bayyana cewa juyin mulki yanzu kusan ya zama ba zai yiwu ba a Najeriya saboda fahimtar dimokuradiyya cikin sojoji
  • Ya ce horo da kwarewar da aka ba jami’an soja tun bayan mulkin Shugaba Janar Ibrahim Babangida sun canja tunaninsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon daraktan yada labarai na sojoji, Janar John Enenche mai rataya ya yi magana kan yiwuwar samun juyin mulki a Najeriya.

Enenche ya ce juyin mulki yanzu kusan “ba zai yiwu ba” saboda tsarin tunani a rundunar soji wanda zai wahala a kifar da gwamnatin farar hula.

Tsohon Janar ya magantu kan yiwuwar juyin mulki a Najeriya
Tsohon Janar a Najeriya, John Enenche. Hoto: HQ Nigeria Army.
Source: Facebook

Tsohon soja ya yi magana kan juyin mulki

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Tinubu zai tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin

Yayin hira da Channels TV, Enenche ya ce jita-jitar juyin mulki ba ta dame shi sosai ba inda ya jaddada cewa sabon tsari da aka dora jami’an sojoji baya goyon bayan kifar da gwamnati.

Ya ce horo da koyarwar da rundunar soji ta samu shekaru 30 da suka gabata sun bayyana cewa gwamnatin soja ba ta dace ba kuma ba ta amfanar ma’aikata.

Ya tunatar da cewa rundunar soji ta sha wahala a zamanin mulkin soja, inda kayayyaki, jin dadi da ci gaban cibiyoyi suka tsaya gaba daya a wancan lokacin.

Enenche ya ce irin wadannan abubuwa sun canja tunanin jami’an soja na yau, suna ganin shiga siyasa ba abu ne mai amfani ga rundunar ko kasa ba.

Ya nuna cewa juyin mulki ya fi yawa a wasu kasashen Yammacin Afirka saboda rashin zurfin dimokuradiyya da tarihi mai cike da matsalolin siyasa da tasirin mulkin mallaka.

An farantawa Tinubu game da yiwuwar juyin mulki a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

'Kasashen da ake samun juyin mulki'

Tsohon janar din ya ce mafi yawan kasashen da ke fuskantar juyin mulki rainon Faransa ne, inda ake ganin rashin gamsuwa da tasirin kasashen Turai tun bayan samun ‘yanci.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi bayani game da jirgi da sojinta da ke tsare a Kasar Burkina Faso

Ya yi misali da Mali wacce kusan ta katse hulda da Faransa, yana cewa irin wannan yanayi ya nuna dalilin da yasa rainon Ingila ba su cika shiga juyin mulki ba.

Duk da cewa ba ya ganin juyin mulki zai yiwu a Najeriya, ya gargadi cewa rikici a makwabtan kasashe zai iya shafar tsaro, tattalin arziki da harkokin kasuwanci.

Ya ce barazanar rikicewa a Benin ko sauran kasashe na iya jawo durkushewar kasuwanci da yawaitar hijira zuwa Najeriya kamar yadda aka gani a Libya.

Tinubu zai tura sojoji Jamhuriyar Benin

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya samu amincewar Majalisar Dattawa domin daukar mataki mai tsauri a Jamhuriyar Benin da suke makwabtaka.

Hakan ya biyo bayan yunkurin juyin mulki da aka yi a kasar wanda bai yi nasara ba a ranar Lahadi 7 ga watan Disambar 2025 wanda yan tawaye suka yi a kasar.

Tinubu ya ce Benin ta nemi tallafin jiragen yaki na Najeriya, domin dakile barazanar yan tawaye da ke neman rusa dimokuraɗiyya wanda ya ce ba zai lamunci haka ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.