Juyin Mulki: 'Matakin da Tinubu Ya Dauka a Benin Ya Dakile Barazanar da Ta Tunkaro Najeriya'

Juyin Mulki: 'Matakin da Tinubu Ya Dauka a Benin Ya Dakile Barazanar da Ta Tunkaro Najeriya'

  • Gwamnonin Najeriya sun ce matakin da Shugaba Tinubu ya dauka na dakile juyin mulki a Jamhuriyar Benin ya ceci Najeriya
  • Shugaban kungiyar gwamnoni (NGF) kuma gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ne ya bayyana haka, ya yaba wa Bola Tinubu
  • Najeriya ta taimaka wajen wargaza shirin sojoji na karbe mulki a Jamhuriyar Benin, wacce ke makwatfaka da kasar nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara, Nigeria - Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun jinjinawa shugaban masa, Bola Ahmed Tinubu bisa matakin gaggawa da ya dauka na dakile yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin.

Gwamnonin karkashin kungiyarsu ta NGF sun yaba wa Bola Tinubu, suna mai cewa hakan ya dakile baranazar da ka iya tunakaro Najeriya idan juyin mulkin ya tabbata.

Gwamnan Kwara.
Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq Hoto: @AARahman
Source: Facebook

A rahoton Daily Trust, gwamnonin sun ce gaggawar da Tinubu ya yi wajen dakile yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin ya hana aukuwar babbar barazana ga tsaron Najeriya.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Majalisa ta cimma matsaya kan bukatar Tinubu ta tura sojoji zuwa Benin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban NGF kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ne ya bayyana haka a wata sanarwa yayin da yake martani kan abin da ya faru a Benin, mai makwaftaka da Najeriya.

Wace baranzana Tinubu ya dakile?

Gwamna AbdulRazaq ya ce da sojoji sun yi nasara, hakan zai ba ‘yan bindiga da kungiyoyin ta’addanci da ke yawo a yankin Sahel damar shiga Benin da kuma kara matsin lamba ga Najeriya.

Ya ce tunu an cika yawancin yankunan Benin, ciki har da dajin W, da makaman kungiyoyin tayar da tarzoma, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.

A cewarsa, kowane irin tabarbarewar tsarin mulki a ƙasar da ke makwaftaka da Najeriya kamar Benin zai shafi yankuna da kan iyakalokin kasar nan kai tsaye.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ya ce:

“Baya ga kare tsarin dimokuraɗiyya a Benin, Shugaba Tinubu ya yi aiki ne don amfanin Najeriya da yammacin Afirka baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Benin: Bidiyon 'yan tawaye na harbin jirgin yaki da Tinubu ya tura kasar

"Idan da an yi nasarar juyin mulki a Benin, sakamakon da zai biyo baya na iya zama mai tsanani ga Najeriya saboda doguwar iyakan da muke da ita da ƙasar.”

Gwamnoni sun yabawa sojojin Najeriya

Kungiyar NGF ta kuma jinjinawa rundunar sojojin Najeriya bisa gaggawar da suka yi wajen taimakawa wjanentabbatar da zaman lafiya a Benin.

A cewarta, kowace barazana da ta shafi manyan biranen Kamhuriyar Benin irin su Porto Novo, Kwatano ko Parakou, barazana ce ga Najeriya.

Kungiyar gwamnonin Najeriya.
Gwamnonin jihohin Najeriya yayin da sune gudanar da taro a Abuja Hoto: @AARahman
Source: Facebook

Gwamnonin sun ce:

“Dimokuraɗiyya, duk tana da ƙalubale, ita ce tsarin da ya fi tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaba.”

A karshe, NGF ta ce wannan mataki ya karfafa kokarin ECOWAS na hana yaduwar ta’addanci da rikice-rikice a yankin Sahel da yammacin Afirka.

Tinubu zai tura sojoji zuwa Jamhuriyar Benin

A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na tura dakarun sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin.

Majalisar ta amince a tura dakarun ne domin tallafa wa kokarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan yunkurin juyin mulki da aka yi a kasar.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Tinubu zai tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin

Duka sanatocin da suka halarci zaman Majalisar Dattawa a yau Talata, sun kada kuri’an goyon baya, wanda hakan ya bada cikakken izini na tura sojoji domin wanzar da zaman lafiya a Benin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262