Gaskiyar abin da Ya Faru a Lamurde, Garin da Ake Zargin Sojoji Sun Kashe Mata
- Rundunar sojojin Najeriya ta 23 Brigade ta ce ba ta da hannu a mutuwar wasu mata biyu da aka ce an harbe su har lahira a jihar Adamawa
- Wata sanarwar rundunar 23 Brigade tace tawagar kwamandan rundunar ko 'yan rakiyarsa ba su je wurin da aka ce an yi harbe-harben ba
- Rundunar ta jaddada cewa wasu 'yan bindiga ne da ke goyon bayan daya daga cikin kabilun da ake rikici da su ne suka kashe matan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Adamawa - Hedikwatar rundunar sojojin kasa ta 23 Brigade ta musanta rahotannin da ake yadawa cewa sojojinta sun bude wa fararen hula wuta a jihar Adamawa.
Rundunar 23 Brigade ta ce ko kusa, babu wani hadin sojojinta da rikicin al'umma da ya barke a karamar hukumar Lamurde da ke jihar a ranar Litinin, 8 ga Disamba, 2025.

Source: Twitter
Adamawa: Sojoji sun karyata harbin fararen hula
Karyata wadannan rahotanni na kunshe a sanarwar da mataimakin daraktan watsa labarai na Sector 4 Operation Hadin Kai / 23 Brigade, Kyaftin Olusegun Abidoye ya fitar a shafin rundunar na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata, Kyaftin Abidoye ya ce babu kamshin gaskiya a rahotannin da ake yadawa kuma kamandan rundunar ko masu yi masa rakiya ba su a wurin da abin ya faru lokacin da aka ce an yi harbe-harben.
"Kwamadan ya na ganawa da babban hafsan sojin kasa ta yanar gizo, inda yake ba da rahoton ayyukan rundunar na mako-mako, a lokacin da aka ce abin ya faru."
- Kyaftin Olusegun Abidoye.
Sanarwar ta bayyana cewa dakarun hadin gwiwa da suka hada da sojojin 23 Brigade, 'yan sanda, NSCDC, da DSS, sun kai dauki a lokacin da suka samu rahoton rikici ya barke tsakanin kabilun Bachama da Chobo kan wani fili.
Musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan bindiga
Sanarwar ta ce dakarun tsaron sun isa garuruwan da rikicin ya shafa, da suka hada da Tingno, Rigange, Tito, Waduku, da Lamurde, domin wanzar da zaman lafiya.
"An ce wannan rikicin ya faru ne saboda wata rigimar gona da kabilun suka jima suna yi, kuma sojoji da sauran jami'an tsaro sun je garuruwan Tingno, Rigange, Tito, Waduku, da Lamurde don kwantar da tarzoma."
- Kyaftin Olusegun Abidoye.
A yayin da jami'an suka je garuruwan kwantar da tarzoma, Kyaftin Abidoye ya ce wasu 'yan bindiga da ake zargin suna goyon bayan kabila daya suka bude wa sojojin wuta.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
"A musayar wutar da aka yi, sojoji suka kashe 'yan bindiga uku, sannan aka sake gano wasu 'yan bindigar a wata hanya da suka bi don su tsere, aka kashe su."

Source: Twitter
Abin da ya jawo aka kashe mata 2
Sanarwar ta kuma a lokacin da suka samu rahoto cewa an kai hari sakatariyar karamar hukumar Lamurde, sojoji sun isa wurin don kwantar da tarzoma, in ji rahoton Punch.
A nan ne rundunar ta ce wasu mata suka yi yunkurin hana sojojin wucewa, kuma wasu 'yan bindiga suka bude wuta kan mai uwa da wabe.
Rundunar ta tabbatar da cewa babu wani farar hula da sojoji suka harba, kuma 'yan bindigar da suka yi harbi ne suka kashe mata biyu da aka kai gawarsu gidan gwamnatin karamar hukumar
Sojojin sun kashe 'yan ta'adda
A wani labari, mun ruwaito cewa, sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara a makonni biyu da suka gabata, inda suka kashe 'yan ta'adda da dama.
Baya ga 'yan ta'addan da aka kashe, dakarun sojojin sun kuma samu damar ceto mutum 67 da aka sace, tare da kama wasu 94 da ake zargi da aikata laifuffuka.
A Arewa maso Gabas, sojojin Operation Hadin Kai sun ci gaba da fatattakar Boko Haram da ISWAP a Borno da Adamawa, inda suka hallaka ‘yan ta’adda da dama.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


