Da Gaske Sojojin Najeriya Sun Harbe Mata Masu Zanga Zanga har Lahira a Adamawa?
- Rundunar Sojin Najeriya ta ce rahoton cewa jami’anta sun harbi mata a lokacin zanga-zanga a Lamurde ba gaskiya ba ne
- Ta bayyana cewa kwamandan rundunar ma bai kasance a wajen rikicin ba, domin yana cikin wani taro ta yanar gizo a lokacin
- Sojojin sun ce matsalar ta samo asali ne daga rikicin ƙabilu tsakanin Chobo da Bachama, inda aka kai wa wasu dakaru farmaki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Adamawa – Rundunar sojin Najeriya ta karyata wani rahoton da ya zargi dakarunta da harbin mata masu zanga-zanga a Lamurde, jihar Adamawa.
A cewar sanarwar rundunar, an yi ƙoƙarin ɓata sunan dakarunta ne, tare da ƙoƙarin nuna wa jama’a cewa sojoji ne suka haifar da asarar rayuka, alhali “ba haka lamarin yake ba kwata-kwata.”

Source: Facebook
Sanarwar da rundunar ta fitar a X ta ce kwamandan rundunar ba ya wajen rikicin lokacin da aka yi zargin harbin matan, domin yana cikin taron mako-mako da babban hafsan soja kasa ta yanar gizo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikici ya jawo an farmaki sojoji a Adamawa
Rundunar ta ce ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 1:30 na dare a ranar 8, Disamba, 2025, cewa rikici ya ɓarke tsakanin ƙabilun Bachama da Chobo a yankunan Tingno, Rigange, Tito, Waduku da Lamurde.
Vanguard ta rahoto cewa rundunar ta bayyana rikicin da cewa ya samo asali ne daga rikicin fili da kuma matsanancin zargi tsakanin al’ummomin biyu.
Dakarun tare da ’yan sanda, NSCDC da DSS sun isa yankin cikin gaggawa domin dakatar da tashin hankalin, sai dai wata ƙungiyar ’yan bindiga da ake zargin na goyon bayan ɗaya daga cikin ɓangarorin ta kai wa sojoji hari.
Sojoji sun mayar da martani a Adamawa
Rundunar ta ce yayin musayar wuta, dakarun suka “yi aiki cikin ƙwarewa,” inda suka kashe uku cikin 'yan ta'addan, sauran kuma suka tsere.
Bayan haka, yayin bin sawun ’yan bindigar, an gano ƙarin mutane biyar da suka rasa rayukansu tare da barin babur ɗaya.

Source: Facebook
Dakarun daga bisani suka samu rahoton cewa wasu daga cikin al’umman da ke yaki sun nufi sakateriyar ƙaramar hukumar Lamurde.
Rundunar soji ta ce ba ta harbi mata a Adamawa ba
A hanyar zuwa Lamurde, rundunar ta ce wasu mata suka tare hanya domin dakatar da sojojin, yayin da wasu ’yan bindiga da ake zargin masu goyon bayan Bachama suka ci gaba da harbi.
A cewar sanarwar:
“Sojoji sun kutsa cikin natsuwa suka wuce zuwa sakateriyar, ba tare da an yi harbi ko an ji wa wata mata ciwo ba. Da akwai harbin da mu ka aikata, babu wata hanya da za mu wuce cikin taron jama’a.”
'Yan bindiga sun bude wuta a cikin kasuwa
A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun bude wuta a wata kasuwa a Anambra.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga kasuwar ne a lokacin da dare ya fara kuma suka fara budewa jama'a wuta.
Wani da ya tsallake rijiya ta baya a harin ya bayyana cewa an kashe mutane da dama sai dai ba a gano adadinsu ba tukuna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


