Rikicin kabilanci ya barke tsakanin yan kasuwa Hausawa da Yarbawa a jahar Ogun

Rikicin kabilanci ya barke tsakanin yan kasuwa Hausawa da Yarbawa a jahar Ogun

Akalla mutane biyu ne suka samu munana rauni sakamakon barkewar rikicin kabilanci tsakanin yan kabilar Hausa da kabilar Yarbawa dake kasuwanci a kasuwar Lafenwa dake garin Abekuta, babban birnin jahar Ogun.

Daily Trust ta ruwaito rikicin ya faru ne a daren Laraba, 12 ga watan Feburairu, kuma ya samo asali ne bayan samun jita jitan mutuwar wani dan kasuwa bahaushe wanda ake zargin masu karbar kudin harajin kasuwa ne suka sare shi.

KU KARANTA: Buhari ya yi alkawarin sake gina gidajen da Boko Haram ta kona a Auno tare da biyan fansa

Majiyarmu ta ruwaito wani dan kasuwa Bahaushe ne ya ki biyan harajin da ake biyan yan iskan gari zauna gari banza a kullum bayan kwashe kusan sa’o’i 10 yana cin kasuwa, hakan ne ya tunzura zauna garin banzan suka sassare shi.

Ganin barnar da suka yi masa ne sai suka ranta ana kare, suka barshi kwance male male cikin jini, rai a hannun Allah. Sai dai mai magana da yawun Yansandan jahar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma yace babu wanda ya mutu a rikicin.

Oyeyemi ya tabbatar da mutane biyu sun jikkata, kuma tuni an garzaya dasu zuwa asibiti domin samun kulawa, sa’annan yace sun kama mutane hudu dake da hannu cikin rikici, haka zalika an tura jami’an Yansanda domin su tabbatar da zaman lafiya a unguwar.

“Mahauta a kasuwar Lafenwa sun dade suna karbar kudi daga yan kasuwan, kudin wurin da suke ajiye hajojinsu, sun tafi amsan kudin kamar yadda suka saba ne sai yan kasuwa Hausawa suka ki biya, daga nan aka fara rikici, har aka sari yan kasuwa Hausawa guda biyu, kuma a yanzu haka suna asibiti.

“An kama mutane hudu dauke da wukake guda 8, za mu tabbata mun hukunta duk wadanda suke da hannu a cikin rikicin, kuma zasu fuskanci fushin doka.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Babban sufetan Yansandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu ya amince da tsarin rundunar tsaro ta yankin Yarbawa, watau Amotekun, bayan gwamnonin jahohin yankin sun rattafa hannu kan tsare tsaren aikin rundunar.

Gwamnonin sun bayyana ma IG Adamu cewa rundunar Amotekun za ta taimaka wajen kare yankin daga ayyukan miyagun mutane, tare da tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu.

Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu SAN ne ya bayyana haka a madadin gwamnonin yankin kudu maso yammacin Najeriya, a yayin taron tsaro na yan doka da babban sufetan Yansandan ya kira a ranar Alhamis a jahar Legas.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: