Tsohon Hadimin Tinubu Ya Kalubalanci Shugaban Kasa game da Takarar 2027
- Tsohon mashawarcin Kashim Shettima kan harkokin tsaro, Hakeem Baba-Ahmed ya sake bayar da shawara ga Bola Tinubu
- Ya ce bai kamata Shugaban Kasa ya rika tunanin sake tsayawa takara ba matukar da gaske ya ke kaunar ci gaban kasar nan
- Dr. Hakeem Baba Ahmed ya bayyana cewa shekaru biyun da rabi da Tinubu ya yi a mulki sun fito da gazawarsa baro-baro
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon ma ba Mataimakin Shugaban Kasa shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba Ahmed ya ba Bola Tinubu shawara game da zaben 2027.
Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake nazari kan ci gaba da rike kujerarsa bayan shekarar 2027.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta wallafa cewa tsohon hadimin Shugaban Kasa ya kara da cewa saukar Tinubu daga mulkin Najeriya zai fi zama alheri da rike kujerar.
Hakeem Baba Ahmed ya shawarci Bola Tinubu
Daily Post ta wallafa cewa Baba-Ahmed ya ce shekaru biyu da rabi da Tinubu ya shafe a mulki sun nuna cewa ba zai iya ba.
Ya bayyana cewa akwai babban gibi tsakanin abin da gwamnati ke cewa tana yi da abin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
A cewarsa, talauci da wahala sun karu, al’umma na cikin halin tsadar rayuwa, kuma matsalolin tsaro sun ta’azzara fiye da yadda aka bar su a mulkin baya.
Ya ce:
“Abin da yake cewa yana yi ya da bambanci da abin da mutane ke gani a yau.”
'Ana wahala a mulkin Tinubu' - Hakeem Baba-Ahmed
Ya kara da cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Najeriya cikin mawuyacin halin tsaro, amma a yanzu ma babu ci gaba.
Hakeem Baba Ahmed ya ce:
“Tinubu bai inganta komai ba; maimakon haka al’amura sun kara tabarbarewa.”
“Idan Shugaba Tinubu na son ganin Najeriya ta tsira, ina ganin lokaci ya yi da zai yi murabus.”

Source: Facebook
Ya ce duk da cewa mulkin dimokuradiyya na ba da damar shugaban kasa ya tsaya takara har sau biyu, al’ummar Najeriya su fara tunanin samun sabon shugaba a shekarar 2027.
Tsohon mai ba da shawarar ya kuma jaddada cewa ci gaban Najeriya ya fi muhimmanci fiye da a bar gwamnati a hannun wanda ba ya kawo sauyi.
A cewarsa, Najeriya tana bukatar shugaba mai kuzari, hangen nesa da dabarun warware matsalolin tsaro, tattalin arziki da jin dadin jama’a.
Hakeem Baba Ahmed ya tabo Atiku
A wani labarin, mun wallafa cewa Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana mahangarsa kan siyasar Najeriya gabanin zaben 2027 da burin neman takarar Atiku Abubakar.
Tsohon hadimin Shugaban Kasan ya shawarci dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da ya sake tunani kan kudirinsa na komawa takara.

Kara karanta wannan
"Akwai abin da ba a karya da shi": Rarara ya fadi dalilin aikin alheri a kauyensu
Ya ce lokaci ya yi da Atiku, wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasa na tsawon shekaru takwas a mulkin Olusegun Obasanjo, ya daina neman shugabanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

