'Dan Majalisar Amurka Mai Sukan Najeriya kan Tsaro Ya Sassauto, Ya Yaba wa Tinubu

'Dan Majalisar Amurka Mai Sukan Najeriya kan Tsaro Ya Sassauto, Ya Yaba wa Tinubu

  • Dan malisar dokokin Amurka Riley Moore ya ce ceto daliban makarantar St. Mary’s da ke Papiri a Neja ya nuna kokarin Bola Tinubu
  • Moore ya bayyana haka ne bayan ganawa da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, a ziyararsa zuwa Najeriya
  • Ya tabbatar da cewa an kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka domin daukar matakai kan kalubalen tsaro

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yaba da nasarar ceto fiye da 100 daga cikin daliban da aka sace daga makarantar St. Mary’s a Neja.

Rahotanni sun nuna cewa an sace ɗaliban ne a Papiri da ke karamar hukumar Agwara ta jihar Neja a watan da ya wuce.

Kara karanta wannan

Zargin kisan kiristoci: Amurka da Najeriya sun fara samun fahimtar juna

Tawagar Amurka da Najeriya a Abuja
Tawagar Amurka yayin ganawa da Ribadu a Abuja. Hoto: @RepRileyMoore
Source: Twitter

A sakon da ya wallafa a X, dan majalisar ya ce ceto daliban ya nuna sababbIn matakan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke dauka wajen yaki da matsalar tsaro a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Moore ya yi wannan tsokaci ne bayan ganawarsa da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, yayin ziyararsa da yake yi a kasar nan.

Ziyarar tasa ta zo ne bayan jita-jita da muhawara mai zafi tsakanin jami’an Amurka da na Najeriya kan rade-radin cin zarafin Kiristoci.

Tattaunawar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka

Jonathan Pratt daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa Amurka za ta yi aiki tare da gwamnatin Najeriya don daukar matakai kan tsaro ciki har da kafa kwamitin hadin gwiwa.

The Cable ta rahoto Moore ya ce kwamitin da aka dade ana tattaunawa a kai, yanzu an kafa shi kuma ya fara aiki gadan-gadan.

'Dan majalisar ya bayyana hakan a matsayin muhimmiyar alama ta kasancewar tsarin hadin gwiwa na tsaro da ke kara karfi tsakanin kasashen.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta cika alkawari, ta ceto daliban makarantar Neja 100 daga ƴan ta'adda

Ya kara da cewa Amurka na daukar batun tsaron Najeriya da muhimmanci, kuma tattaunawarsu da Ribadu ta tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya na shirye ta ba da hadin kai.

'Dan majalisar Amurka ya yabi Najeriya

A cikin sakonsa, Moore ya bayyana cewa tattaunawa tsakaninsa da Ribadu ta samar da muhimman abubuwa da dama da za su iya canza yanayin tsaro a fadin kasar.

Ya ce an tattauna tsare-tsaren da za su taimaka wajen dakile kungiyoyin ta’addanci musamman a yankin Arewa maso Gabas.

Haka kuma ya ce matakan za su taimaka wajen dakatar da kisan mutane a yankin Arewa ta Tsakiya, lamarin da ya ce shi da shugaban Amurka ke da matukar damuwa a kai.

Ribadu da dan majalisar Amurka
Nuhu Ribadu tare dan majalisar Amurka, Riley Moore. Hoto: @RepRileyMoore
Source: Facebook

Moore ya yabawa gwamnatin Najeriya kan yadda ta gudanar da aikin ceto daliban makarantar Katolika da aka sace, yana mai cewa irin wannan nasara na kara karfafa amincewa da jajircewar shugabancin kasar.

Jirgin Najeriya ya makale a Burkina Faso

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin kasar Burkina Faso ta ce ta rike wani jirgin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Kisan Kiristoci': Tawagar Amurka ta shigo Najeriya, ta yi magana da Ribadu

Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan Najeriya ta tura jiragen yaki Benin sun tarwatsa masu yunkurin kifar da gwamnatin ƙasar.

Burkina Faso ta zargi jirgin Najeriya da keta mata sararin samaniya ba tare da izini ba, inda ta ce za ta yi bincike kan hakan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng