ADC Ta Zargi Gwamnati da Sakaci da Tsaron Najeriya bayan Hana Juyin Mulki a Benin

ADC Ta Zargi Gwamnati da Sakaci da Tsaron Najeriya bayan Hana Juyin Mulki a Benin

  • Jam’iyyar ADC ta yaba wa gaggawar da gwamnatin tarayya ta nuna wajen dakile yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin
  • Mai magana yawun jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ya ce amma hakan ya bayyana yadda gwamnati ke jinkirin magance matsalar tsaro a cikin gida
  • ADC mai hamayya ta tambayi dalilin da ya sa gwamnati ba ta nuna irin wannan gaggawa a rikicin Guinea-Bissau da Najeriya ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Jam’iyyar ADC ta jinjinawa gwamnatin tarayya bisa saurin da ta nuna wajen dakile yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin cikingagvawa.

Sai dai jam'iyyar adawa ta yi amfani da damar wajen kiran gwamnati da ta yi amfani da irin wannan zafin nama wajen yaƙi da ta’addanci da garkuwa da mutane a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zargin kisan kiristoci: Amurka da Najeriya sun fara samun fahimtar juna

ADC ta caccaki Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, Bolaji Abdullahi, Kakakin ADC na kasa Hoto: Sanusi Bature D-Tofa/Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC ta yi magana kan aikin Najeriya a Benin

Daily Post ta ruwaito ADC ta ce gaggawar gwamnati a Benin ya nuna cewa akwai ƙarfin iya ɗaukar mataki idan an so a kawo ƙarshen ta'addanci da gaske.

Sanarwar da Bolaji Abdullahi ta ce yanzu abin ya kai ga a tambayi dalilin da ya sa gwamnati ke jinkirta magance rikice-rikicen cikin gida.

Kakakin ADC ya kalubalanci Tinubu kan batun tsaro
Mai magana da ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Mallam Abdullahi ya ce:

“ADC na maraba da gaggawar da Najeriya ta nuna a Benin bayan bayyanar yunƙurin juyin mulki. Mun yaba da yadda gwamnatin tarayya ta hanzarta kare tsarin mulki a maƙwabciyarmu.”

Shawarar ADC ga gwamnatin Najeriya

Sai dai Bolaji Abdullahi ya jaddada cewa dole ne gwamnatin ta nemi amincewar Majalisar Dokoki idan za a tura jami’an tsaro wajen ƙasar waje.

Kara karanta wannan

ECOWAS ta tura zaratan sojoji Benin daga Najeriya da wasu kasashe 3

Jam’iyyar adawa ta kuma tuna da yadda gwamnati ta yi jinkiri a lokacin rikicin Guinea-Bissau, duk da cewa wani tsohon shugaban Najeriya ya makale a lokacin tashin hankalin.

Ta ce wannan bambancin ya haifar da tambayar me ya canza? Menene ke sa Najeriya ta yi gaggawa a wasu lokuta, amma ta yi shiru a wasu?

ADC ta yi gargadi cewa rashin daidaito a yadda Najeriya ke shiga lamarin ƙasashen waje yana iya rage tasirinta a yankin, musamman idan ana maganar kare dimokuraɗiyya.

Jam’iyyar ta ce akwai rade-radin cewa wata ƙasa mai ƙarfi daga waje ta taka rawa a lamarin Benin, abin da ke kara haifar da shakku game da gaskiyar matakin.

ADC ta ce:

“Idan za mu iya daukar mataki cikin sauri a Benin, me ya sa ba mu iya irin wannan gaggawa a kan ta’addanci, garkuwa da mutane da kashe-kashe da ke addabar al’ummominmu?"

ADC ta dura a kan gwamnatin Tinubu

A baya, mun ruwaito cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu game da matakin da ta dauka a kan rikicin Ministan Abuja da wani jami'in sojan ruwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dauki matakai 3 bayan sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Benin

Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana damuwarsa kan yadda Gwamnatin Tarayya ta yi shiru game da takaddamar da ta shiga tsakanin Nyesom Wike da Laftanar A.M Yerima.

A cewar Abdullahi, an kwashe kusan awanni 48 bayan bidiyon da ya nuna Wike yana cacar baki da jami’in rundunar sojan ruwan, amma gwamnati ta yi gum.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng