Manyan Kasa za Su Taru domin Kaddamar da Littafi da Taron Tuna Buhari na Farko
- Za a gabatar da littafin da Lai Mohammed ya rubuta domin tunawa da ranar haihuwar marigayi Muhammadu Buhari a 17, Disamba, 2025
- Manyan jami’an gwamnati da shugabannin gargajiya za su halarci taron da za a yi a dakin taron Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja
- An bayyana cewa littafin ya kunshi tarihin mulki, sadarwa da manufofin gwamnati a lokacin da Muhammadu Buhari ya shugabanci Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – A ranar 17, Disamba, 2025, za a yi bikin gabatar da wani sabon littafi da Alhaji Lai Mohammed ya rubuta domin tunawa da ranar haihuwar marigayi Muhammadu Buhari, wanda da yana da rai zai cika shekaru 83.
Buhari ya rasu ne a ranar 13, Yuli, 2025, kuma wannan shi ne karo na farko da za a yi taron zagayowar ranar haihuwarsa bayan rasuwarsa.

Source: Facebook
Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya wallafa a X cewa littafin mai suna Headlines & Soundbites: Media Moments that Defined an Administration ya ƙunshi tarihin aikin gwamnati da dabarun sadarwa a shekarun mulkin Buhari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabanni da manyan baƙin da za su hallara
Shugaban taron shi ne tsohon gwamnan jihar Osun, Bisi Akande, wanda kuma shi ne shugaban rikon kwarya na farko na jam’iyyar APC.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III tare da sauran sarakunan gargajiya daga faɗin ƙasar nan za su hallara.
An sanar da cewa matar marigayin tsohon shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari za ta kasance a wajen gagarumin taron da za a yi.
Daga cikin manyan ‘yan kasuwa da za su taka rawa a matsayin masu kaddamarwa akwai Alhaji Aliko Dangote; Alhaji Abdulsamad Rabiu; Sardaunan Dutse, Alhaji Nasiru Danu; Dr Kesington Adebutu; da kuma Aare Kola Oyefeso.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa za a gudanar da taron ne da misalin ƙarfe 10:00am na safe a dakin taron Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja.
Mahimmancin littafin tuna Buhari da aka rubuta
A yayin magana kan littafin, Lai Mohammed ya bayyana cewa manufar sa ita ce tunatar da al’umma tarihin rayuwa da hidimar marigayi Buhari, da kuma nazarin manufofin da suka jagoranci gwamnatin sa tsawon shekaru takwas.
Ya ce littafin ya tattara abubuwan da suka shafi sadarwa da dabarun gwamnatin da suka taka rawa wajen kafa manufofin kasa.

Source: Facebook
Littafin ya kuma yi bayani kan irin nauyin da ma’aikatar yada labarai da al’adu ta ɗauka a lokacin mulkin Muhammadu Buhari.
An ce taron yana ɗaya daga cikin manyan abubuwan da aka shirya domin karrama tsohon shugaban ƙasar da kuma tunatar da al’umma irin rawar da ya taka a tarihin Najeriya.
Wata mata ta yi mafarkin Muhammadu Buhari
A wani labarin, mun kawo muku cewa wata mata da ake kira Baby Buhari ta bayyanna cewa ta yi mafarkin Muhammadu Buhari.
A cikin bayanan da ta yi, matar ta ce ta kalli tsohon shugaban kasar sanye da wasu fararen kaya a wani waje yana zaune.
Baya ga haka, matar ta kara da cewa ya mata godiya da irin addu'o'in da take masa, inda ta ce ya ce 'na gode da addu'a."
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


