Ibrahim Traoré na Burkina Faso Ya Rike Sojojin Najeriya da Jirginsu a Kasar Shi
- An tilasta wa jirgin sojin Najeriya sauka a Bobo Dioulasso bayan matuƙin ya fuskanci matsala a cikin sararin samaniyar Burkina Faso
- Hukumar kasashen Sahel ta AES ta ce bincike ya nuna babu wanda ya ba jirgin izinin ketare Burkina Faso, lamarin da ta kira take hakki
- Sai dai har yanzu gwamnati da rundunar sojin saman Najeriya ba su fitar da sanarwa ba kan abin da ya faru da sojojin da ke cikin jirgin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Burkina Faso ta ce ta tilasta wa wani jirgin rundunar sojin saman Najeriya sauka a garin Bobo Dioulasso bayan zargin cewa ya shiga sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 8, Disamba, 2025, lokacin da jirgin ya samu matsalar gaggawa a sama.

Source: Facebook
Mai sharhi kan tsaro a Afrika, Brant Philip ya wallafa a X cewa gwamnatin Burkina Faso ta rike dakarun Najeriya 11 da ke cikin jirgin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
AES ta bayyana takaicinta kan abin da ta kira karya dokar sararin samaniya, tare da shawartar kasashe mambobinta su kasance cikin shiri na musamman idan anyi yunkurin zarcewa cikin sararin samaniyarsu.
An rike jirgin Najeriya a Burkina Faso
A cewar bayanin AES, jirgin C130 na rundunar sojin saman Najeriya ya shiga cikin sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da cikakken izini ba.
Hukumar ta ce binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa ba a samu takardar izinin wucewa ba, duk da cewa jirgin ya nemi sauka saboda “matsalar gaggawa” da ya fuskanta a sama.
Rahoton da jaridar Punch ta wallafa ya nuna cewa an ce jirgin ya ƙunshi mutum 11 – ma’aikatan jirgi guda biyu da sauran jami’an soja tara.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta dauki matakai 3 bayan sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Benin
Bayan an tilasta masa sauka, hukumomin Burkina Faso sun shaida cewa an fara gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin dalilin ketarewa ba tare da umarni ba.
AES ta yi kakkausar suka, tana mai cewa duk wani yunkurin karya dokokin sararin samaniya na yankin za a ɗauke shi a matsayin take hakkin kasa.

Source: Twitter
Martanin AES da gargadin kare sararin samaniya
AES ta bayyana cewa take hakkin kasashen yankin ya ci karo da abin da ta ce rashin bin ka’idojin ketare sama da jirgin sojin Najeriya ya yi.
Kungiyar ta yi nuni da cewa an umarci rundunonin tsaro masu kare sararin samaniya su kasance cikin shiri domin tsare duk wani jirgi da zai karya dokokin yankin.
Wannan matakin ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, musamman ganin cewa babu wata sanarwa daga gwamnatin Najeriya.
Najeriya ta tura jirgin yaki kasar Benin
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta tabbatar da tura jiragen yaki kasar Benin domin tarwatsa masu shirin juyin mulki.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa kasar Benin ce ta nemi agajin Najeriya yayin da sojoji suka so kifar da gwamnati.
Bayan nasarar da sojojin Najeriya suka yi wajen fatattakar masu shirin juya mulkin, Bola Tinubu ya jinjina musu, inda ya ce sun yi kokari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
