Zargin Kisan Kiristoci: Amurka da Najeriya Sun Fara Samun Fahimtar Juna

Zargin Kisan Kiristoci: Amurka da Najeriya Sun Fara Samun Fahimtar Juna

  • Dan majalisar Amurka Riley Moore ya ce ganawarsa da Nuhu Ribadu ta buɗe sabuwar kofar fahimtar juna
  • Riley Moore ya jawo tawagar Amurka zuwa Najeriya bayan ƙasarsa ta kafe a kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
  • Gwamnatin Najeriya kuma ta ƙaryata zargin, sai dai ta tabbatar da cewa ana fama da matsalolin tsaro masu tarin yawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Dan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, wanda ya shahara wajen caccakar gwamnatin Najeriya kan batun kisan Kiristoci ya gana da Mashawarcin Shugaban Ƙasa, Nuhu Ribadu.

Ya bayyana cewa ganawarsa da Nuhu Ribadu ta buɗe sabuwar kofar fahimtar juna kuma an samu sakamako mai kyau da zai tabbatar da haɗin kan ƙasashen biyu.

Kara karanta wannan

Bulama Bukarti ya bada shawara bayan shigowar tawagar Amurka Najeriya

Dan majalisar Amurka ya faɗi sakamakon zama da Nuhu Ribadu
Mashawarcin Shugaban Najeriya, Nuhu Ribadu tare da Riley Moore Hoto: Rabi'u Biyora
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa sakamako Moore na cikin tawagar ‘yan majalisar Amurka da ke ziyarar Najeriya domin tattauna batutuwan tsaro da rikice-rikice a yammacin Afrika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan Majalisar Amurka ya gana da Nuhu Ribadu

Punch ta ruwaito Moore ya ce matakai da shirye-shiryen da aka tattauna tsakaninsa da jami’an gwamnati, wadanda idan aka aiwatar da su za su inganta tsaro ga dukkanin ‘yan Najeriya.

Moore ya ce ana samun fahimtar juna da Najeriya Hoto: Buhari Sallau
Riley Moore yayin gaisawa da Nuhu Ribadu Hoto: Buhari Sallau
Source: Facebook

Ya kara da cewa damuwar Amurka game da rikice-rikicen Najeriya ta samu karɓuwa, yana yabawa gwamnati saboda bisa yadda ta amince a tattauna game da matsalar.

Moore ya ce ya kamata wannan fahimta ta zo aikace, yana mai cewa akwai sauran aiki mai yawa, amma abubuwa na tafiya a hanya turbar da ta dace.

Martanin Ribadu bayan Moore ya zo Najeriya

A nasa bangaren, Nuhu Ribadu ya wallafa cewa tattaunawar ta mai da hankali kan yaƙi da ta’addanci, tabbatar da zaman lafiyar yanki.

Kara karanta wannan

'Kisan Kiristoci': Tawagar Amurka ta shigo Najeriya, ta yi magana da Ribadu

Haka kuma sun kara magana sosai a kan ƙarfafa dangantakar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya domin samar da zaman lafiya mai dorewa.

Ya ce yana da yakinin cewa wannan ganawa za ta kara gina amincewa da haɗin gwiwa domin samun zaman lafiya da tsaro.

Kafin wannan ganawar, Riley Moore shi ne ya fi tsananta kira da a hukunta Najeriya a Amurka, tun kafin Donald Trump ya sanya ta a cikin jerin kasashen da ake da damuwa ta musamman a kansu (CPC).

Moore ya taba rubuta wasika ga Sakataren Harkokin Waje, inda ya nemi amfani da dukkanin dabarun diflomasiyya domin tunkarar abin da ya kira “kisan Kirista” a Najeriya.

Ya kuma danganta laifuffukan Boko Haram, Ansaru da ISIS-WA da hare-haren da ke faruwa, sannan ya ce akwai rahotannin da ke zargin wasu miyagun jami’an gwamnati da hannu a cikin rikice-rikicen

Bukarti ya shawarci tawagar Amurka

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen lauya kuma mai sharhi a harkokin tsaro, Bulama Bukarti, ya buƙaci tawagar majalisar dokokin Amurka ta ziyarci Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Suna da manyan makamai,' Sheikh Gumi ya ce ana taimakon 'yan ta'adda daga ketare

Bukarti ya bukaci tawagar su zagaya garuruwa da kauyuka domin su gani da idonsu yadda ‘yan Musulmi da Kiristoci ke zaune tare, a kasuwanni, asibitoci da sauran wurare.

A cewar Bukarti, ganin yadda mutane ke rayuwa a kullum zai taimaka wajen tantance hakikanin yanayin — idan akwai kisan kare-dangi ko wariya kan addini ko akasin haka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng