'Na Gama Yin Shiru,' Matawalle Ya Tona Wadanda Ke Daukar Nauyin Bata Masa Suna

'Na Gama Yin Shiru,' Matawalle Ya Tona Wadanda Ke Daukar Nauyin Bata Masa Suna

  • Bello Matawalle ya ce munanan kalamai da ake furtawa kansa siyasa ce kawai, saboda wasu na son bata masa suna da karkatar da hankalinsa
  • Karamin ministan tsaro ya bayyana cewa shi ma ya gaji matsalar ’yan bindiga ne a Zamfara, kuma gwamnatinsa ta rage ta sosai
  • Matawalle ya ce wasu manyan 'yan siyasa ne ke daukar nauyin wadanda ke aibata shi, kuma lokaci ya yi da zai fara mayar da matarni

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Bello Matawalle, karamin ministan tsaro ya ce masu sukarsa na yin haka ne kawai domin biyan bukatun kansu saboda sauyin matsalar tsaro da ake samu.

Mai magana da yawun ministan tsaron Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 8 ga Disamba, 2025.

Kara karanta wannan

Bidiyon da ya sa wasu 'yan Najeriya ke neman sai Matawalle ya yi murabus

Bello Matawalle ya yi martani ga wadanda ke sukarsa.
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. Hoto: @Bellomatawalle1
Source: Facebook

Matawalle ya yi martani ga masu sukarsa

A cikin sanarwar, Matawalle ya ce yana fuskantar jerin hare-haren kalaman baki, da ake yi da nufin nuna gazawarsa da kuma adawa da kokarin da yake kan magance matsalar tsaro, in ji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Aikin gwamnati, musamman a kasar da take fuskantar matsalolin tsaro masu girma, na bukatar karfin gwiwa, jajurcewa da kuma riko da gaskiya.
"A cikin 'yan makonnin nan, ina kallon yadda ake yada maganganun karya a kaina, ana jifa ta da kazafi, kuma na san wanna aikin abokan hamayyata ne na siyasa.
"Wadannan mutanen, da hassada ta cika zuciyarsu saboda wata manufar siyasa, sun yi kokarin siyasantar da tsaron kasa, don cimma muradunsu kawai."

- Bello Matawalle.

Matawalle ya ce wadanda ke daukar nauyin sukarsa da ake yi sun kasance wasu fitattun 'yan siyasa da ke neman gindin zama da kuma son karkatar da hankalinsa daga ayyukan da yake yi.

Kara karanta wannan

Albishir da ministan tsaro ya fara yi ga 'yan Najeriya bayan shiga ofis a Abuja

"Wadannan zarge-zargen duk da suke yi ba su da tushe. Kawai siyasa ce. Gaskiya a bayyane take. Na koma gefe ina kallon yadda 'yan siyasa ke cin mutuncina, suna mun kage. Amma lokaci ya yi da zan yi martani."

- Bello Matawalle.

'Gadon matsalar tsaro na yi a Zamfara' - Matawalle

Ya ce matsalar 'yan bindiga matsala ce da ya gaje ta a lokacin yana gwamnan Zamfara kuma gwamnatinsa ta yi amfani da tsari mai kyau na magance matsalolin.

Ministan ya ce:

"Ba a karkashin mulkina ne 'yan bindiga suka shiga Zamfara ba. Ni ma na tarar da matsalar lokacin mulkina, matsala ce da ta dade tana ciwa gwamnatoci tuwo a kwarya.
"Amma amatsayi na na gwamna, ban kyale abun haka ba. Mun samar da tsare-tsare masu karfi don magance matsalolin, yayin da muke aiki kafa-da-kafada da gwamnatin tarayya, sarakuna da jami'an tsaro."

A hannu daya kuma, Matawalle ya ce gwamnatinsa ta samar da kwamitocin tsaro, tsarin tsaro mai inganci da kuma hanyoyin magance matsalar 'yan ta'adda da barayin ma'adanai.

Bello Matawalle ya ce manyan 'yan siyasa ne ke daukar nauyin masu bata masa suna
Bello Matawalle, karamin ministan tsaro yana magana da manema labarai. Hoto: @Bellomatawalle1
Source: Instagram

Kokarin Matawalle na magance matsalar tsaro

Ministan ya ce sai da ta kai ya kori sarakunan gargajiya da ke da hannu a ayyukan ta'addanci sannan ya kawo shirye-shiryen yaki da 'yan bindiga ta hanyar hadin gwiwa da sojoji.

Kara karanta wannan

Kuɗin da yawa: Gwamna Zulum ya faɗi biliyoyin Naira da ya kashe kan tsaro a 2025

A lokacin da yake gwamna, Matawalle ya ce an ceto dubunnan mutane da aka sace kuma an kama tare da mayar da 'yan China 11 da ke satar ma'adanai zuwa kasarsu.

"Wadannan ayyukan sun isa su zama hujja. Duk wanda ke adawa da hakan to yana yi ne kawai don siyasa, yana wasa da hankalin talakawa."

- Bello Matawalle.

Matawalle ya ce Zamfara ta shafe shekara ba tare da wata babbar matsalar tsaro ba saboda matakan da gwamnatinsa suka dauka.

An bukaci Tinubu ya tsige Matawalle

A wani labarin, mun ruwaito cewa, daruruwam mata da maza daga Zamfara sun bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta korar Bello Matawalle daga kujerar minista.

A yayin wata zanga-zanga a hedikwatar DSS a Abuja, wasu mazauna Zamfara sun nuna rashin jin daɗi game da matsalar tsaro da ta addabi jihar.

Masu zanga zangar sun yi ikirari cewa alaƙar Matawalle da ‘yan bindigar a lokacin mulkinsa tana daga cikin dalilan da suka haifar da ƙarin matsalar tsaro a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com