Sojoji Sun Toshe Kofofin Tsira ga 'Yan Bindiga a Sokoto, an Hallaka Tsageru

Sojoji Sun Toshe Kofofin Tsira ga 'Yan Bindiga a Sokoto, an Hallaka Tsageru

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani mugun nufi na 'yan bindiga a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Sojojin sun kubutar da 'yan kasuwan da 'yan bindiga suka yi wa kwanton bauna lokacin da suke kan hanyar zuwa neman na abinci
  • Jami'an tsaron sun yi raga-raga da 'yan bindigan inda suka hallaka wasu daga cikinsu tare da kwato babura da bindigogi a hannunsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Dakarun sojoji sun kashe wasu da ake zargin ’yan bindiga ne yayin wani artabu a jihar Sokoto.

Sojoji sun hallaka 'yan bindigan ne bayan kai dauki don ceto ’yan kasuwa da aka yi wa kwanton-bauna a kan hanyar Tarah–Karawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Sokoto
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce 'yan kasuwar na cikin tafiya daga kauyen Tarah zuwa kasuwar mako ta Sabon Birni ne maharan suka tare su a Kwanan Akimbo da misalin karfe 8:00 na safe.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kai mummunan hari garuruwan Fulani 4 a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Sokoto

Wasu mazauna yankin sun ce sojojin da ke sansaninsu a garin Kurawa sun ji harbe-harbe, inda suka yi gaggawar isa wurin, lamarin da ya jawo musayar wuta wadda ta ɗauki kusan awa guda.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa sun kirga gawarwakin 'yan bindigan da sojojin suka kashe.

“Sojoji sun yi artabu da su sosai. Daga baya ’yan bindigar suka ja da baya suka gudu zuwa maboyarsu a bayan rafi."
"Mun kirga gawarwakin 'yan bindiga tara a nan cikin yankinmu, sannan an sake samun wasu huɗu a cikin daji da gefen rafin.”
“Sojoji sun kwashe makamai da babura da yawa daga wurin, suka tafi da su Kurawa.”

- Wata majiya

Ya kara da cewa mutane biyu ne suka ji rauni daga bangaren fararen hula kuma suna karɓar magani a asibiti, amma an ceto dukkan ’yan kasuwar cikin koshin lafiya ba tare da wani lahani ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mota dauke da 'yan firamare ta yi hatsari, ta afka cikin teku

Hakazalika ya bayyana cewa babu wani soja da ya ji rauni a bangaren jami'amn tsaron.

An gano gawarwakin 'yan bindiga

Da yake tabbatar da lamarin, dan majalisar jiha mai wakiltar Sabon Birni, Hon. Aminu Boza, ya ce an gano gawarwaki akalla tara da ake zargin na maharan ne, kuma ana ci gaba da bincike a yankin.

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original
“An samu makamai da babura da yawa daga hannunsu. Ina fatan sojojinmu za su ci gaba da wannan kokarin."

- Aminu Boza

Wannan hari dai ya faru ne kwana ɗaya bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari a kauyukan Gatawa da Shalla a Sabon Birni da Isa, inda suka kashe mutane guda bakwai tare da yin garkuwa da mata da dama.

'Yan bindiga sun kai hari a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wani kauyen jihar Sokoto.

Yan bindigan sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da mutane 15, ciki har da wasu mata huɗu masu shayarwa da jariransu a harin da suka kai a kauyen Kurawa.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano

Dan majalisar da ke wakiltar yankin, Hon. Sa’idu Ibrahim, ya ce mutum 15 ne maharan suka tafi da su yayin harin da suka kawo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng