Gwamna Radda Ya Jagoranci Tawaga Ta Musamman zuwa Gidan Sheikh Dahiru Bauchi
- Malam Dikko Radda ya jagoranci tawagar manyan jiga-jigai daga Katsina zuwa wurin ta'aziyyar rasuwar Sheikh Dahuru Usman Bauchi
- Gwamna Radda ya yi wa iyalan babban jigon darikar Tijjaniyya ta'aziyya tare da addu'ar Allah Ya jikansa, Ya kuma sanya shi a gidan Aljannah
- Kakakin Majalisar Dokokin Katsina, Rt. Hon. Nasir Daura da Ministan Harkokin Gidaje, Ahmed Dangiwa na cikin tawagar Gwamna Dikko Radda
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina , Nigeria - Bayan kusan makonni biyu da rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, manyan mutane na ci gaba da zuwa har gida domin yiwa iyalan babban malamin ta'aziyya.
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina, wanda bai samu halartar jana'iza ba, ya jagoranci babbar tawaga zuwa Bauchi domin yi wa iyalan marigayin ta'aziyya.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed ya tabbatar da hakan a a wata sanarwa da ya wallafa shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A gidan marigayin, Mataimakin Gwamnan Bauchi, Mohammed Auwal Jatau, tare da wasu jami'an gwamnati sun tarbi tawagar Katsina.
Dikko Radda ya yi wa marigayin addu'a
A bangaren iyalan marigayin kuma, Khalifan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, shi ne ya karɓi gwamnan tare da sauran manyan malamai.
Gwamna Radda ya bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi ga musulmai da Najeriya baki ɗaya, yana mai cewa marigayin ya bar gagarumin gadon ilimi da jagoranci.
An gudanar da addu’o’i domin Allah Ya gafarta masa, Ya saka shi cikin Aljannatul Firdausi, Ya kuma bai wa iyalansa juriya da hakurin rashin da suka yi.
Gwamna Dikko Radda ya shiga cikin gida, ya ziyarci matan marigayin ɗaya bayan ɗaya, domin yi masu ta’aziyya tare da alkawarin ci gaba da taimaka masu.
Jiga-jigan da ke cikin tawagar Katsina
Manyan kusoshin da ke cikin tawagar gwamnan Katsina sun hada da Kakakin Majalisar Dokokin Katsina, Hon. Nasir Yahaya Daura da Ministan Harkokin Gidaje, Ahmad Musa Dangiwa.
Sauran sun kunshi shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Katsina, Abdulkadir Mamman Nasir, sakataren gwamna na kai da kai, Abdullahi Aliyu Turaji da Kwamishinan Harkokin Addini, Ishaq Shehu Dabai.
Limamin Masallacin Juma’a na Katsina, Sheikh Yahaya Musa, Manyan limaman Katsina da Daura da wasu Mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar Katsina sun je ta'aziyya.

Source: Facebook
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu ranar 27 ga Nuwamba 2025, yana da shekaru fiye da dari a kalandar musulunci, bayan shafe kusan shekaru 70 yana wa’azi da koyarwa.
Sanusi II ya je ta'aziyya a Bauchi
A baya, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya ba da uzuri kan rashin halartar jana'izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Basarake ya ziyarci jihar Bauchi tare da manyan ’yan Tijjaniyya da suka take masa baya, kuma ya bayyana cewa ya turo hakimai su halarci sallar jana’iza duk da cewa bai ya kasar.
Sanusi II ya ce Sheikh Dahiru ya bar tarihin tausayi, zaman lafiya, koyi da kyawawan halaye da koyar da Musulunci cikin hikima da natsuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
