Gwamnoni 6 Sun Dura Fadar Aso Rock, Sun Shiga Ganawa da Shugaba Tinubu
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jam'iyyar APC shida a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja a ranar Litinin
- Gwamnonin da suka halarci wannan ganawa sun hada da Ahmad Aliyu (Sokoto), Lucky Aiyedatiwa (Ondo) da kuma Umar Namadi (Jigawa)
- Jihohin Kebbi, Sokoto da Kogi, da gwamnoninsu suka sanya labule da Tinubu sun fuskanci hare-haren 'yan bindiga a 'yan watannin nan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rahotanni da ke shigo mana na nuni da cewa wasu gwamnoni shida na jam'iyyar APC sun dura fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Rahoton ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya shiga ganawar sirri da gwamnonin bayan isarsu fadarsa, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a bayan fage.

Source: Twitter
Gwamnonin sun shiga ofishin shugaban kasa da misalin karfe 4:00 na yammacin yau Litinin, 8 ga watan Disamba, 2025 kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.
An kuma rahoto cewa Tinubu da gwamnonin APC shida ba su shafe awa daya a wannan taron ba, kuma ba a yi wa 'yan jaridar fadar shugaban kasa wani bayani ba.
Har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, Legit Hausa ba ta samu bayani game da makusin wannan taron ba.
Amma mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar da sanarwa game da ganawar a shafinsa na X.
Bayo Onanuga ya ce:
"Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu, gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, gwamnan Jigawa, Umar Namadi, gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris, gwamnan Kogi, Ahmed Usman Ododo da gwamnan Edo, Monday Okpebholo a fadar shugaban kasa."
Tinubu ya dauki matakai kan tsaro
Jaridar Punch ta rahoto cewa wannan taron na zuwa ne yayin da Najeriya ta fuskanci sababbin matsalolin tsaro, ciki har da sace daliban makarantu, masu ibada a Arewa maso Yamma da ta Tsakiya, wadanda aka ceto su daga baya.
Jihohi da dama, kamar Kebbi, Sokoto da Kogi, da gwamnoninsu suka halarci zaman sun fuskanci hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a 'yan watannin nan.
A ranar 26 ga Nuwamba, 2026 Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan tsaro a wani mataki na dakile yawaitar hare-haren 'yan ta'adda a sassan kasar.
Sannan Tinubu ya ba sojoji, 'yan sanda da hukumomin leken asiri umarnin kara yawan wadanda za a dauka aiki da tura dakaru da yawa a jihohin da ke fuskantar hare-hare.

Source: Twitter
Gwamnoni sun yi gum bayan ganawa da Tinubu
Ya kuma bukaci jami'an tsaro da su ba da fifiko a tsaron makarantu, gonaki da wuraren ibada, yayin da gwamnonin jihohi suka dauki nasu matakan kariya.
Hakazalika, an samu sauyin Ministan tsaro a makon jiya, da kuma neman taimako daga kasashen waje don yaki da ta'addanci a Najeriya.
Ko da 'yan jaridar da ke dauko rahoto a fadar shugaban kasa suka tare su bayan kammala wannan zama, gwamnonin ba su ce uffan a kai ba.
Gwamnoni 19 za su tara N19bn duk wata
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun yunkuro da nufin kawo kashen matsalar tsaron da ta addabi al'ummar yankin gaba daya.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, wanda zanta da 'yan jarida ya ce sun amince kowane gwamna zai rika ba da Naira biliyan daya a kowane wata.
Ya ce za a yi amfani da kudin wajen samar da kayan aiki na zamani, daukar matasa 'yan sa-kai da sauran matakan yaki da matsalar tsaro a Arewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


