Shekaru 15 ana Abu 1: Obasanjo Ya Fadi Hanyar Kawar da Boko Haram
- Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwa kan rikicin Boko Haram da ya kai shekaru 15 ana gwabzawa
- Ya bayyana cewa shekarun da aka shafe ana yaki da Boko Haram ya haura wanda aka yi ana yakin basasa daga 1967-1970
- Obasanjo ya ce rundunar sojin Najeriya za ta iya kawar da wannan barazana matukar aka dauki wadansu matakai na musamman
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun – Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bayyana damuwarsa ranar Lahadi kan yadda rikicin Boko Haram ya ki ci, ya ki cinyewa.
Ya bayyana takaicin yadda aka kwashe shekaru15 ana yakin Boko Haram, wanda ya fi tsawon yaki basasa da aka yi daga 1967 zuwa 1970.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa Obasanjo ya yi wannan bayani ne ta yanar gizo a shirin Toyin Falola Interviews.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obasanhjo na takaicin yakin Boko Haram
Jaridar Leadership ta ruwaito Obasanjo ya bayyana cewa rundunar tsaro ta Najeriya tana horo ne don yaki na al’ada, ba don rikicin da ke faruwa a yau ba.
Ya ce akwai bukatar rundunar ta sake taku, sannan a tabbata dakarunta sun samu horo na musamman da ya dace da halin da ake ciki.

Source: Facebook
Shugaban ya tunatar da yadda a shekarar 2011 ya kai ziyara Maiduguri don fahimtar asalin Boko Haram.
Ya bayyana cewa a wancan lokaci, shugabannin kungiyar sun bayyana aniyar tattaunawa, amma gwamnati ba ta amsa kiran ba.
Obasanjo na so a horar da sojoji
Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo ya ce lokaci ya yi Najeriya za ta hada kai da sauran kasashe domin koyo dabarun yaki da barazana irin Boko Haram.
Ya ce:
“Horo shi ne mabuɗin magance wannan matsala. Ana horar da rundunar soji a yanzu da dabaru irin na da, amma barazanar da ake fuskanta yanzu suna rayuwa cikin jama’a ko kuma suna motsi cikin sauri. Wannan na bukatar horo na musamman.”
Ya kara da cewa, Najeriya na bukatar kayan aiki na zamani, tattara bayanai na sirri, da kuma hadin gwiwa da kasashen waje kafin a samu ci gaba mai ma’ana.
Tsohon shugaban ya yi gargadi kan yadda zuba kudi kawai ba ya warware matsalolin tsaro da ci gaban kasa.
Ya kawo misalin wani ɗalibi daga Neja Delta da ya koma aikata ta’addanci saboda rashin aikin yi duk da digiri a fannin 'chemical engineering.'
Ban san shekaru na ba, cewar Obasanjo
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya sake jaddada cewa ba shi da tabbacin ainihin shekarunsa na haihuwa.
Wannan bayani ya fito ne a ranar Lahadi, 7 ga Disamba, 2025, yayin tattaunawa da Farfesa Toyin Falola, tare da Dr. Mathew Kukah da Farfesa Kingsley Moghalu.
Obasanjo ya bayyana cewa yana tantance shekarunsa ne ta hanyar duba shekarun tsofaffin abokansa na makarantar firamare da sakandare da suka rage a duniya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

