Bulama Bukarti Ya Bada Shawara bayan Shigowar Tawagar Amurka Najeriya
- Isowar tawagar majalisar dokokin Amurka ya tayar da sabuwar muhawara kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya
- Mai sharhi a kan al'amuran tsaro, Barista Bulama Bukarti ya bayyana cewa bai kamata tawagar ta tsaya a wuri daya ba
- Ya bayyana bukatar ta ziyarci Arewacin Najeriya inda Musulmi da Kirista ke rayuwa a cikin kwanciyar hankali
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ziyarar tawagar majalisar dokokin Amurka da ta iso Najeriya domin gano gaskiya game da batutuwan tsaro ta haifar da mahawara mai zafi a kasar nan.
A ranar Litinin ne Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya karɓi tawagar, bayan tattaunawar da aka yi a baya a Washington D.C, kasar Amurka.

Source: Facebook
Bayan isowar tawagar ne kuma masanin tsaro kuma mai sharhi a kan harkokin yau da kullum a Najeriya, Barista Bulama Bukarti ya ba wa tawagar shawara a shafinsa na X.
Shawarar Bulama Bukarti ga tawagar Amurka
Fitaccen mai sharhi kan tsaro, kuma mai fafutukar kare hakkin dan adam, Barista Bulama Bukarti, ya yaba da ziyarar, tawagar Amurka zuwa Najeriya, amma ya bukaci a fadada ta zuwa Arewacin kasar gaba ɗaya.

Source: Facebook
Ya ce:
“Ya kamata su zagaya garuruwa da kauyuka, su ga yadda Musulmai da Kiristoci ke rayuwa tare a kasuwanni, asibitoci da wuraren yau da kullum. Idan suka ga hakan, za su iya tantance ko ana kisan kare-dangi ko a’a.”
Bukarti ya jaddada cewa tawagar ta gane wa idanunta yadda 'yan Najeriya ke rayuwa zai fi zama maifi dacewa a kan ta yi amfani da maganganun siyasa kawai.
'Yan Najeriya sun yi martani ga Bulama Bukarti
Wasu masu bibiyar shafin Bulama Bukatar sun yi martani ga kalaman fitaccen lauyan, inda wasu ke ganin tabbas ana kashe kiristocin, kuma maganganun mai fafutukar ya yi ba za su sauya komai ba.
RN Abdulraheem Muh’d ya ce:
“Babu wanda ke cewa Musulmai na kashe Kiristoci. Abin da ake fada shi ne ‘yan bindiga Fulani na kashe Kiristoci, kuma hakan gaskiya ne. Ba za ka musanta cewa mutane a Plateau da Benue su ne manyan wadanda rikice-rikicen suka shafa ba.”
@abbeyResearches ya ce:
“Ka san kona Deborah a Sokoto ya rushe duk abin da kake faɗa a nan. Ƙasa da ba ta iya gurfanar da masu tsattsauran ra’ayin addini a gaban shari’a ba, ba za ta iya cewa ba a samun kisan kare-dangi ko wariyar addini ba.”
Tawagar Amurka ta sauka a Najeriya
A baya, mun wallafa cewa Mashawarcin shugaban ƙasa kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, ya karɓi wata tawaga ta musamman daga Majalisar Dokokin Amurka a Abuja.
Ribadu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 7 ga Disamba, 2025, bayan dawowar tawagarsa daga Amurka kan zargin kisan kiristoci da ganawa da 'yan majalisan.

Kara karanta wannan
Shari'ar Musulunci: MURIC ta kalubalanci Amurka, ta faɗi abin da Musulmi za su yi
A hoton da ya haɗa da rubutun, an ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro yana maraba da tawagar, wanda ya ce ta zo ne domin ci gaba da nazari kan lamarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

