Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Je har Gida, Sun Sace Ɗiyar Babban Malamin Addini

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Je har Gida, Sun Sace Ɗiyar Babban Malamin Addini

  • Rundunar ‘yan sandan Oyo ta tabbatar da cewa an sace Ibukun Otesile, diyar wanda ya kafa cocin Jesus Is King Ministries a gaban gidanta
  • Kungiyar CAN ta bayyana cewa an turo sakon gaggawa cikin daren Alhamis, lamarin da ya tayar da hankalin limamai da Kiristoci a Ibadan
  • CAN ta yi kira ga rundunonin tsaro su dauki mataki cikin gaggawa tare da bukatar a tura karin jami’ai domin tabbatar da kubutar Otesile lafiya

Oyo - Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta tabbatar da cewa an yi garkuwa da shugabar JCI Ibadan Elite ta shekarar 2025, Mrs Ibukun Otesile.

'Yan sanda sun ce wasu gungun 'yan bindiga ne suka yi awon gaba da diyar malamin addinin Kiristan a gaban gidanta da ke General Gas, Akobo, a daren Alhamis.

'Yan sanda sun tabbatar da cewa an sace diyar shugaban cocin Jesus Is King a Ibadan
Kwamishinan 'yan sandan jihar Oyo, CP Femi Haruna. Hoto: @OyoPoliceNG
Source: Twitter

An sace diyar babban malamin Kirista a Oyo

Mai magana da yawun rundunar, SP Adewale Osifeso, ya ce an samu rahoton garkuwar ne da yammacin ranar, kuma tuni jami’ai suka fara aikin gano inda aka kai ta, in ji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa gidan malamin addini a Kaduna da dare, sun sace shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Otesile, wadda ke da yara biyu, ita ce ‘yar Fasto Olalekan Babatunde, wanda shi ne babban limamin Injila kuma wanda ya kafa coci Jesus Is King Ministries da ke Ibadan.

Labarin sace ta ya karade shafukan sada zumunta da safiyar Juma’a, inda ‘yan uwa, abokai da shugabannin addini suka shiga tururuwa da kira ga hukumomi su gaggauta daukar mataki.

A cewar Olamide Olanrewaju, mataimakin shugaban CAN a jihar Oyo, kungiyar ta samu sakon gaggawa kusan karfe 8:45 na dare, lokacin da aka sanar da cewa an yi awon gaba da ‘yar Reverend Babatunde.

Lokacin da aka sace diyar faston a kofar gida

Ya bayyana cewa a cikin dandalinsu na WhatsApp, limamai suka fara addu’a, sai dai ya bukaci a hada da daukar matakan tsaro da sanar da hukumomin da suka dace domin a ceci wadda aka a kan cikin lokaci.

Olanrewaju ya ce sun tabbatar daga bayanan da suka samu cewa an tare Otesile ne a kofar gidanta lokacin da ta je shiga, sannan aka tilasta mata shiga mota kafin a yi awon gaba da ita.

Kara karanta wannan

Kasa ta rikice: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da kusa a APC

A cikin sanarwar gaggawa da CAN ta raba, kungiyar ta bayyana cewa Otesile ta fada hannun masu garkuwa da mutane ne da misalin karfe 8:00 na daren Alhamis.

Sun bayyana damuwa matuka tare da kira ga al’ummar jihar su ci gaba da addu’a domin kare lafiyarta da dawowarta gida lafiya, in ji rahoton The Nation.

Kungiyar CAN ta roki jami'an tsaro su gaggauta ceto diyar shugaban cocin Jesus Is King na Ibadan
Taswirar jihar Oyo, inda aka sace diyar wanda ya kafa cocin Jesus Is King, Ibadan. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun fadi halin da ake ciki

A halin yanzu, kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta yi kira ga rundunonin tsaro wadanda suka hada da Hedikwatar Rundunar Sojin Najeriya da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya su dauki matakan gaggawa domin kubutar da Otesile.

Kungiyar ta ce lamarin ya zama wani sabon kalubale ga tsarin tsaro na jihar, musamman ganin cewa an sace matar ne a unguwar da ake ganin tana da tsaro sosai.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da cewa tana gudanar da aikin tattara bayanai tare da binciken kwararru na EOD da sauran sassa.

A cewar rundunar, hakan zai sa a gano wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da ceto ta. Har yanzu ba a fitar da bayanin neman kudin fansa ko dalilin sace ta ba.

Kara karanta wannan

Allah sarki: Mata, miji da 'ya'yansu duka sun kone yayin gobara a Katsina

'Yan bindiga sun sace fasto a Kaduna

A wani labari, mun ruwaito cewa, hankulan al'umma sun tashi matuka bayan harin yan bindiga a gidan malamin addinin Kirista a jihar Kaduna.

‘Yan bindiga sun sace faston Katolika mai suna Emmanuel Ezema, wanda ke hidima a cocin St. Peter’s da ke unguwar Rumi, cikin jihar Kaduna.

Ana ci gaba da kiran gwamnatin tarayya da ta yi kokarin kawo karshen hare-haren yan bindiga domin samun zaman lafiya da kare dukiyoyin al'umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com