'Ku Daina Sayen Motocin Alfarma,' Muhimmin Sakon Dangote ga Masu Kudi a Najeriya

'Ku Daina Sayen Motocin Alfarma,' Muhimmin Sakon Dangote ga Masu Kudi a Najeriya

  • Alhaji Aliko Dangote ya ce kashe kuɗaɗe wajen sayen motoci masu tsada da jiragen sama na alfarma yana tauye ci gaban Najeriya
  • Ya bayyana cewa Najeriya na kara yawan jama’a da miliyoyin jarirai duk shekara, wanda ke bukatar wutar lantarki, masana’antu
  • Dangote ya jaddada cewa masu kudi daga waje ba za su zuba jari a Najeriya ba, har sai masu kudin kasar sun dauki wasu matakai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yi kira ga manyan ’yan Najeriya da su rage kashe makudan kuɗaɗensu a kan abubuwan alfarma kamar motoci masu tsada da jiragen sama.

Maimakon sayen motoci da jiragen alfarma don amfanin kai, Dangote ya yi kira ga 'yan Najeriya da su mayar da hankali wajen gina masana’antu da samar da ayyukan yi.

Kara karanta wannan

Cikakkun sunayen jakadun kasashe 21 da suka mika wa Tinubu takardu a Abuja

Alhaji Aliko Dangote ya yi magana kan zuba jari a Najeriya
Alhaji Aliko Dangote, yana jawabi a wani taro da kamfanin Dangote ya shirya. Hoto: @DangoteGroup
Source: Getty Images

Dangote ya nemi a rage sayen motocin alfarma

Dangote ya yi wannan jawabi ne bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a Aso Rock, ranar Asabar, inda ya ce almubazzaranci ya zama babban gibi wajen ci gaban kasarnan, in ji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tuna yadda a zamanin mulkin soja, shugabanni har ma da shugaban kasa ke hawa Peugeot 504 a matsayin babbar mota, yana mai cewa hakan ya takaita nuna bambanci a zamantakewa.

"Idan ka kalli tsarin Najeriya a can baya, lokacin mulkin soja, daga kan shugaban kasa zuwa kasa, kowa na amfani da Peugeot 504. Ita ce mota mafi girman amfani a lokacin.
"Don haka, idan shugaban kasa yana amfani da Peugeot 504, kai a matsayinka na mai kudi ko dan kasuwa, ko ma wanene kai, ba za ka zo kana hawa Rolls-Royce ba."

- Alhaji Aliko Dangote.

Damuwar Dangote kan sayen jiragen masu kudi

Kara karanta wannan

"Ya tafi har abada": Dangote ya yi wa 'yan Najeriya sabon albishir

Dangote ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda filayen jiragen saman kasar, musamman Abuja da Legas, suka cika da jiragen masu kudi.

A cewar fitaccen dan kasuwar, kuɗin da ake kashewa wajen saye da kula da wadannan jirage zai iya kafa masana’antu da samar da dubban ayyukan yi a cikin gida.

Dangote ya ce tattalin arzikin Najeriya ba zai taba tashi ba muddin ba a mayar da hankali kan masana’antu, noma da cigaban masana’antar sarrafa kayayyaki ba.

Dangote ya ce akwai bukatar a gina masana'antu a Najeriya.
Matatar Dangote da attajirin Afrika, Aliko Dangote ya gina a Legas. Hoto: Bloomberg
Source: UGC

Shawarar Dangote ga gwamnati da 'yan Najeriya

A cewar Dagote, ƙasar Najeriya na fuskantar babbar matsala ta yawan jama’a, inda ake samun karin jarirai kimanin miliyan 8.7 a duk shekara, in ji rahoton Leadership.

Dangote ya ce wannan karuwar na bukatar wutar lantarki mai dorewa, gine-gine na ilimi da lafiya da ingantacciyar hanyar samar da ayyukan yi ga matasa.

Dangote ya kuma yi suka kan dogaro da gwamnatin Najeriya ke yi da masu zuba jari na kasashen waje. A cewarsa, babu wani babban dan kasar waje da zai zuba jari a Najeriya muddin ’yan cikin kasar ba su fara zuba jari ba da kansu.

Kara karanta wannan

"Akwai abin da ba a karya da shi": Rarara ya fadi dalilin aikin alheri a kauyensu

Ya jaddada cewa manufarsa ita ce ganin Najeriya ta samu ci gaba ta hanyar masana’antu da kamfanonin sarrafa kayayyaki da ’yan kasuwa na cikin gida suka gina.

Dangote ya yi albishir ga 'yan Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban matatar Dangote, Aliko Dangote, ya yi magana kan samar da isashshen man fetur a Najeriya.

Dangote ya nuna cewa matatar man da yake da ita a Legas ta magance matsalar da 'yan Najeriya suka dade suna fama da ita shekara da shekaru.

Ya kuma ce sun rubuta takarda ga Hukumar NMDPRA don sanar da ita cewa yanzu za su iya samar da lita miliyan 50 na man fetur kullum a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com