Farfesa Aminu Dorayi: Bakanon da ya tuko motarsa daga Landan har zuwa Kano
- Farfesa Aminu Dorayi, wani malami a jami'a ya kafa babban tarihi a rayuwarsa ta duniya
- An ruwaito yadda malamin ya tuko mota daga Landan har Najeriya cikin 'yan kwanaki
- Hakazalika, an rahoto yadda malamin ya ki aikin karantarwa a Amurka domin ya koyar a Kano
Farfesa Aminu Mohammed Dorayi ba kawai cikakken dan boko bane mai zurfin karatu kuma dattijon kasa, idan ana maganar tarihi, ya kafa tarihi mai kyau da ban al'ajabi a rayuwarsa wanda ba za a iya mantawa ba.
Abusites sun ruwaito cewa Farfesa Aminu wanda ya taba kasancewa Shugaban Gwamnatin Kungiyar Dalibai na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya taba wata tafiya daga birnin London har zuwa babban birnin Kano shekaru da yawa da suka gabata da motarsa.
Farfesan dan asalin jihar Kano, a cikin wata hira da Daily Trust a 2019 ya ba da labarin yadda ya yi tafiyar wacce ta dauke shi kwanaki 24 a cikin motarsa kirar Peugeot 504.
Kwanaki nawa ya yi a hanya?
Da yake tunawa da tafiyar tasa mai cike da tarihi, Auto Josh ya ba da rahoton cewa, farfesan da ake wa lakabi da 'The Adventurous Chemist' ya ce ya yi tafiyar ta hanyar ke ta hamada.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“... Na tuka mota ta hanyar Paris haka nan ta Madrid, Gibraltar. Don haka lokacin da ka isa Gibraltar, ka isa Tekun Bahar Rum, inda kuma za ka shiga jirgin ruwa zuwa Aljeriya.
"Daga can ka shiga hanya ta ko'ina, ko da yake babu hanya, a cikin hamada, jagorar ka, taswirar ka."
Ya aje aikin koyarwa a Amurka saboda ya dawo Najeriya ya karantar
Aminu wanda ya yi karatun firamare a jihar Kano an kuma ce shi ya shirya baje kolin kasuwanci na farko a Najeriya.
Bayan kammala karatunsa na PhD a Amurka yana dan shekara 30, dattijon ya yi watsi da ayyukan koyarwa da yawa a Amurka domin ya dawo Kano ya karantar da al'ummarsa.
Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa
Masani: Malaman Najeriya za su iya gogayya da kowane irin malami a duniya
A wani labarin, Yayin da ake ci gaba da kokarin ganin an daukaka darajar aikin koyarwa, da alama akwai kyakkyawan fata ga kowane malamin makaranta a Najeriya.
A wata hira ta musamman da Legit.ng ta yi da Ebere Anyanwu, alkalin shirin TV na Naija Teacher's Reality ya bayyana cewa babban makasudin shirin shine samar da gogaggu kuma kwararrun malamai wadanda zasu yi tasiri kan ilimi ga yaran Najeriya.
Asali: Legit.ng