Iyalai Za Su Ɗasa, Shettima Ya Kaddamar da Shirin Tallafin N1bn ga Ƴan Kasuwa
- Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya kaddamar da tallafin Naira biliyan ɗaya ga iyalai domin dogaro da kansu
- Shirin zai karfafa kananan yan kasuwa kuma ya rage talauci kai tsaye duba da halin da ake ciki na matsin tattalin arziki
- Kashim ya yaba da haɗin kan gwamnatin tarayya da ta jiha, yana cewa tsarin ya dace da manufar Renewed Hope da ARISE wajen samar da ayyuka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwa Ibom - Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya kaddamar da shirin tallafin kasuwanci ga ƙananan yan kasuwa.
Tallafin ya kai Naira biliyan ɗaya a Ukanafun/Oruk Anam a Akwa Ibom, yana mai cewa gwamnati dole ta kai arzikinta ga kowane mataki.

Source: Twitter
Iyalai 3,000 sun samu tallafin kudi
Hakan na cikin wata sanarwa da Mai taimaka masa, Stanley Nkwocha wanda ya wallafa a shafin X a yau Asabar 6 ga watan Disambar 2025.

Kara karanta wannan
'Suna da manyan makamai,' Sheikh Gumi ya ce ana taimakon 'yan ta'adda daga ketare
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shirin wanda Hon. Unyime Idem ya kirkiro, yana bai wa iyalai kudin faɗaɗa kasuwancinsu.
Shettima ya ce gwamnatin Tinubu na goyon bayan ci gaban jama’a kai tsaye domin inganta al'umma.
Ya jaddada cewa ci gaba mai ɗorewa yana faruwa ne idan ‘yan ƙasa sun samu dama su zama masu kirkire-kirkire inda ya ce wannan shi ne sahihin tallafi.
Ya bayyana dacewar shirin da ajandar Renewed Hope, musamman batutuwan samar da ayyukan yi, rage talauci, tallafa wa kananan yan kasuwa.
Mataimakin Shugaban Ƙasa ya kara da cewa dimokuradiyya tana yin tasiri idan alkawuran gwamnati sun isa iyalai a ƙasa, suna ba su ƙarfi da damar kasuwanci.
Ya yaba da haɗin kan gwamnatin tarayya da ta Akwa Ibom, yana yabon ajandar ARISE ta Gwamna Umo Eno, wadda ta mayar da hankali kan noma da ci gaban karkara.

Source: Twitter
Amfanin da iyalai za su samu da tallafin
Shettima ya ce tsarin tallafin iyali zai ƙara yawan sana’o’i, ya bunƙasa kuɗaɗen shiga, ya ƙarfafa matasa da mata, tare da rage dogaro da wasu.
Ya shawarci masu cin gajiyar su yi amfani da jarin yadda ya kamata, saboda yana da damar haifar da ci gaban zuri’a inda ya ce za a ɗauki kowa a matakai na gaba.
Mataimakiyar Gwamna, Sanata Akon Eyakenyi, ta godewa Shettima bisa halartar taron, tana cewa ana daukar sa a matsayin ɗan uwa a jihar, saboda irin goyon bayansa.
Hon. Unyime Idem ya ce iyalai 3,000 sun amfana cikin adalci yana mai cewa shirin ya nuna cikakkiyar dacewa tsakanin tsarin tarayya da ta jiha don amfanin mutane.
Gwamnati za ta fadada tallafin N25,000
Kun ji cewa Gwamnatin tarayya za ta fadada shirin tallafawa magidanta masu karamin karfi na CCT bayan sama da mutane miliyan 5 sun amfana.
Karamin ministan harkokin jin kai, Dr. Yusuf Tanko Sununu ya ce za a kara daukar mutane 600,000 a fadin jihohin Najeriya.
A karkashin shirin CCT, kowane mai cin gajiya yana samun tallafin kudi N25,000 daga gwamnatin tarayya na tsawon watanni uku.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
