An Samu Matsala: Jirgin Saman Sojojin Najeriya Ya Yi Hatsari a Jihar Neja
- Wani jirgin sama na rundunar sojojin Najeriya ya gamu da hatsari a kusa da Karabonde, cikin Karamar Hukumar Borgu ta jihar Neja
- Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa matukan jirgin sun samu nasarar fita lafiya tun kafin jirgin ya kife da yammacin yau Asabar
- Rundunar sojojin sama ba ta ce komai ba kawo yammacin na yau amma an fara yada bidiyoyin yadda jirgin ya kama da wuta bayan hatsarin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Rahotanni daga jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya sun nuna cewa wani jirgin rundunar sojojin sama (NAF) ya gamu da hatsari.
Bayanai sun nuna cewa jirgin yakin sojojin ya fado kasa tare da kamawa da wuta a kusa da Karabonde, cikin Karamar Hukumar Borgu ta jihar Neja.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu ya 'wawure' Naira biliyan 16.5 na gyaran gadar Arewa? Gaskiya ta fito

Source: Original
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa matukan jirgin biyu sun tsira bayan sun yi amfani da rigar sauka ta gaggawa kafin jirgin ya fadi kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani gidan talabijin na yanar gizo da ke jihar Neja, Lapai TV, ya wallafa faifan bidiyon wurin da jirgin ya yi hatsari a shafinsa na Facebook da yammacin yau Asabar.
Yadda jirgin sojoji ya fado a Neja
Wani ganau ya shaida wa jaridar ta hanyar sakon murya cewa matukan jirgin sun samu nasarar fita lafiya kafin jirgin ya yi ƙasa da ya fadi da karfi.
Ya ce:
“Muna tsammanin jirgin ya taso ne daga sansanin sojin sama na Kainji. Bayan aukuwar lamarin mun fahimci jami'an sojojin sama sun fara tattaki zuwa wurin hatsarin.”
A wata tattaunawa ta waya, wani mazaunin yankin mai suna Lukman Sulaiman ya ce hatsarin jirgin sojojin Najeriya ya faru ne misalin karfe 4:10 na yamma.
"Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:10 na yamma. Jirgin ya fado ne kusa da gari amma Allah Ya kiyaye, matukan jirgin sun yi nasarar ficewa lafiya," in ji shi.
Halin da mutane suka shiga bayan hatsarin
Da aka tambaye shi ko matukan jirgin ba su ji rauni ba, ya ce, "Eh, mun ji karar fadowar jirgi mai kara da karfi, mun tsorata, amma daga ƙarshe muka fara tafiya zuwa wurin da abin ya faru."
Ya kara da cewa jama’a sun firgita da karar fashewar da suka ji kafin su fara mamaye wajen da lamarin ya faru.

Source: Twitter
Bidiyoyi biyu da ake yadawa sun nuna jirgin Alpha Jet ɗin yana ƙonewa a cikin daji bayan ya fadi.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, rundunar sojin saman Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa game da hatsarin ba.
Jiragen sojoji sun yi luguden wuta a Neja
A wani rahoton, kun ji cewa jiragen sojoji sun samu nasarar hallaka daya daga cikin manyan jagororin 'yan bindiga da suka addabi al'umma a jihar Neja.
Luguden wutan jiargen sojojin Najeriya ya hallaka Babangida, ɗaya daga cikin sanannun kwamandojin ’yan bindiga a karamar hukumar Shiroro.
An ce mutuwar Babangida ta raunana dabar Dogo Gide, wanda ya shahara wajen kai hare-hare masu tsanani a sassan Jihar Neja da makwabtan jihohi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

