Sunan Buratai Ya Fito cikin Masu ‘Daukar’ Nauyin Ta’addanci, Ya Yi Martani
- Tsohon hafsan sojojin kasa a Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya magantu bayan saka sunansa cikin zargin taimakon ta'addanci
- Buratai ya yi karin haske ne kan zargin da ke cewa yana da hannun kai tsaye ko kaikaice wajen daukar nauyin ta’addanci
- Akwai mutane da dama ciki har da tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari da ake zarginsu da wannan mummunan laifi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Hafsan Hafsoshin Sojoji, Tukur Yusuf Buratai ya fito ya karyata jita-jita da ake yadawa kansa game da ta'addanci.
Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya ya karyata rade-radin da aka danganta shi da batun daukar nauyin ta’addanci, kai tsaye ko kaikaice.

Source: Twitter
Tukur Buratai ya musanta alaka da ta'addanci
Buratai ya fadi haka ne a wata sanarwa da aka fitar a madadinsa daga bakin tsohon kakakin rundunar sojin kasa, Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman mai ritaya da ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
Malami: Tsohon ministan Buhari ya dau zafi bayan an zarge shi da daukar nauyin ta'addanci
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wannan zargi karya ne tsagwaronta, babu wani tushe, kuma gaba daya an kirkire shi ne domin bata masa.
Hakan ya biyo bayan wata kafar yanar gizo ta wallafa rahoto da ke danganta manyan mutane da masu daukar nauyin ta’addanci.
A cewarsa, a duk tsawon aikinsa, ba a taba kiran sa, bincikar sa, ko alakanta shi da irin wannan batu ba daga kowace hukuma ko cibiyar tsaro ba.
Babu hukumar leken asiri, gidan shari’a, ofishin jakadanci, ko majalisar duba aikace-aikace da ta taba danganta shi da ta’addanci.

Source: Facebook
Wadanda suka alakanta Buratai da ta'addanci
Sanarwar ta bayyana cewa Sahara Reporters ta jingina labarin ne da ikrarin da ba a tantance ba na Janar Danjuma Ali-Keffi mai ritaya wanda Buratai ya ce wannan labari “shirme ne babu ma’ana, babu hujja, kuma cike yake da sharri.”
Ya ce abin takaici ne, amma ba sabon abu ba, ganin cewa kafar ta saba yunkurin bata masa suna tun da dadewa, duk da cewa kullum basu cin nasara saboda aikinsa ya kasance bayyananne, tsarkakakke, kuma cike da girmamawa ga kasa.
Sanarwar ta tunatar da cewa Tukur Buratai ya shafe fiye da shekaru 40 yana hidima da kishin kasa, inda karkashin jagorancinsa aka fatattaki Boko Haram da ISWAP.
“Abin ba shi da ma’ana kuma ya sabawa hankali, a danganta wanda ya yi tsayin daka wajen yaki da ta’addanci da duk wani lamari da ya shafi tallafawa ‘yan ta’adda."
- Cewar sanarwar
Daga karshe, sanarwar ta nemi Sahara Reporters da Janar Ali-Keffi su janye kalamansu tare da bada hakuri a bainar jama’a.
Malami ya musanta alaka da ta'addanci
An ji cewa tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya yi tsokaci bayan an ambaci sunansa cikin mutanen da ake zargi da alaka da ta'addanci.
Malami SAN ya bayyana cewa ko sau daya ba a taba gayyatarsa a ciki ko wajen Najeriya kan batun da ya shafi daukar nauyin ta'addanci ba.
Tsohon ministan wanda ya kasance babban lauyan gwamnati ya bayyana manufar da mutanen da ke yada zargin daukar nauyin ta'addancin ke son cimmawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
