Bidiyon da Ya Sa Wasu ’Yan Najeriya Ke Neman Sai Matawalle Ya Yi Murabus

Bidiyon da Ya Sa Wasu ’Yan Najeriya Ke Neman Sai Matawalle Ya Yi Murabus

  • Wasu yan Najeriya sun sake dawo da wani tsohon bidiyon karamin ministan tsaro, Bello Matawalle na 2021
  • A bidiyon an ji Matawalle yana kare wasu ’yan bindiga abin da ya jawo haifar da kiraye-kirayen ya yi murabus
  • Masu sharhi a kafafen sadarwa sun ce ba zai yiwu mai nuna tausayi ga ’yan ta’adda ya zama Ministan tsaro ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An kuma samun wasu dalilai da yasa ’yan Najeriya ke ganin ya kamata Bello Matawalle ya yi murabus daga kujerar da yake kai.

Masu amfani da kafofin sadarwa sun taso Bello Matawalle a gaba bayan tsohon bidiyonsa ya sake bayyana wanda ya jawo maganganu.

An sake taso Matawalle a gaba ya yi murabus
Tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Source: Original

An sake taso Matawalle a gaba kan murabus

Rahoton Vanguard ta ce hakan bai rasa nasaba da matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya da ya sa kowa ya zaku a kawo sauyi.

Kara karanta wannan

An buga rikici da Matawalle a ma'aikatar tsaro kafin Badaru ya ajiye aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon bidiyon na Matawalle ya sake bayyana kusan lokacin da Ministan tsaro, Mohammed Badaru ya yi murabus.

Bidiyon da aka fito da shi tun shekarar 2021 yana nuna tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, yana kare wasu ’yan bindiga da ke tada tarzoma a jiharsa.

Bidiyon ya nuna Matawalle yana cewa:

“Ba dukkansu ne ’yan ta’adda ba. Idan ka bincika, wasu lokuta ana zaluntar su ne da sunan ’yan sa-kai. Ana kai musu farmaki, ana kwace musu dabbobi, babu wanda ke magana a madadinsu, suna ramawa ne kawai.
"Ba dukkansu ne mugaye ba, wasu ’yan kasa nagari ne, amma yanayi ya tura su aikata laifi.”

An ce ya yi wannan magana ne a Fadar Shugaban Kasa bayan ganawa da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ana zargin Matawalle da alaka da yan ta'adda
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. Hoto: Defence Headquaters Nigeria.
Source: Original

Martanin mutane game da kalaman Matawalle

'Yan Najeriya da dama na kira da a tilasta masa murabus saboda bidiyon, suna cewa babu dalilin da zai sa mai kare ’yan ta’adda ya rike mukami a gwamnati, balle ma a ma’aikatar tsaro.

Kara karanta wannan

Albishir da ministan tsaro ya fara yi ga 'yan Najeriya bayan shiga ofis a Abuja

Shafin Rock Yusuf TV da ya wallafa a YouTube da taken cewa da gaske Matawalle na da alaka da yan bindiga?

Akinyemi Lofindipe ya rubuta:

“Tsohon bidiyo ko sabo, yaya mutum mai irin wannan tunani zai zama ministan tsaro?”

Francis Afolayan ya ce:

“Kana cewa mutum dan ta’adda ne amma har yanzu kana kiransa nagari. Wani irin jagoranci muka shiga?”

Jacob Kenny Idowu ya kara da cewa:

“Wannan mutumin mai tausayin ’yan bindiga ne. Ba za mu ci nasara a yakin nan da irin shi a ma’aikatar tsaro ba. Babu wani uzuri da zai sa mutum ya aikata laifi.”

Abin da ya fi muni shi ne yadda bidiyon ya tayar da zargin cewa wai ministan yana da alaka da shugabannin ’yan bindiga domin tabbatar da nasarar APC a 2027.

A X, @ehiralp7 ya rubuta:

“Najeriya abin mamaki. Ka yi tunanin irin wannan magana a talabijin, shi ya sa rashin tsaro ke ci gaba.”

@paugodwin967 ya kara cewa:

“Ka ji irin maganar da mutumin nan yake yi! Rashin tsaro, satar mutane, duk suna cewa wani sashe ne na abin?”

Kara karanta wannan

'Suna da manyan makamai,' Sheikh Gumi ya ce ana taimakon 'yan ta'adda daga ketare

@chudilingo4438 ma ya rubuta cewa:

“Sun fi samun bayanai fiye da sojoji. Kalli jerin mutanen da ke kula da tsaron mu, da yawa ana zargin su da tallafawa Boko Haram."

Matawalle: 'Yan Kudu sun roki Tinubu alfarma

An ji cewa kungiyar NDYC ta yi magana game da tasirin da Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ke da shi a gwamnatin Bola Tinubu.

Wannan kungiya daga Kudancin Najeria ta roƙi Tinubu ya ƙi amincewa da yunkurin batanci da ake yi wa Matawalle.

Ta ce maganganun suna fitowa ne daga masu tsoron tasirin Matawalle a siyasar Arewa da goyon bayan Tinubu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.