Gwamnatin Kano Ta Yi Magana bayan Kama Tsohon Shugaban PCACC, Muhuyi Magaji
- Gwamnatin Kano ta nuna damuwa kan yadda aka tura dakarun 'yan sanda dauke da makamai suka tafi da Muhuyi Magaji Rimin Gado
- 'Yan sanda sun cafke tsohon shugaban hukumar PCACC a jiya Juma'a yayin wani samame da suka kai ofishinsa a titin Zaria, Kano
- A wata sanarwa, kwamishinan shari'a na Kano ya koka kan yadda aka kama Rimin Gado ba tare da tuntubar gwamnatin Kano ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnatin Jihar Kano ta yi martani tare da nuna damuwarta kan kama tsohon shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci (PCACC) na jihar, Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Da yammacin kiya Juma'a ne wasu dakarun 'yan sanda da suka ce daga birnin tarayya Abuja aka ba su umarni, suka cafke Rimin Gado a ofishinsa da ke cikin birnin Kano.

Source: Twitter
Leadership ta rahoto cewa gwamnatin Kano ta nuna damuwarta a wata sanarwar da Kwamishinan Shari’a kuma Antoni Janar na jihar, Barista Abdulkarim Kabiru Maude SAN, ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano ta soki kama Muhuyi Rimin Gado
Gwamnati ta bayyana cewa ta samu labarin kama Rimin Gado “cikin matuƙar damuwa” inda jami’an ‘yan sanda “dauke da manyan makamai” suka yi awon gaba da shi.
Kwamishinan shari'a na Kano ya ce an kama Rimin Gado ne misalin ƙarfe 5:30 na yamma a ofishin lauyansa da ke kan titin Zaria, Kano, “ba tare da nuna masa takardar izinin kamu ko umarnin kotu ba."
Ya ce yadda aka kama Rimin Gado ya nuna akwai wata a kasa duba da tanade-tanaden kundin tsarin mulki na 1999, sashe na 35, 36 da 46 da ke kare ‘yancin mutum, samun adalci da damar zuwa kotu domin kare haƙƙinsa.
“Gwamnatin Kano ba ta jayayya da ikon rundunar ‘yan sanda na binciken laifi, amma dole a yi komai cikin bin doka, kariya ta kundin tsarin mulki da mutunta haƙƙin ɗan ƙasa,” in ji Maude.
Gwamnatin Kano ta fadi illar kama Rimin Gado
Kwamishinan ya ce abin takaici ne yadda aka gudanar da irin wannan aiki kan tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci ba tare da sanarwa ko haɗa kai da bangaren shari'ar Kano ba.
Sannan kwamishinan ya yi gargadin cewa yanayin kamun, musamman yadda aka tura fiye da jami’an ‘yan sanda 40 masu makamai, na iya haifar da tsoro, ruɗani da fassarar siyasa a cikin jihar.
Ya yi zargin cewa, “akwai wasu ‘yan siyasa daga wajen Kano da ke ƙoƙarin amfani da hukumomin tarayya domin tada hankalin jihar Kano.”
Sanarwar ta kara bayyana cewa akwai umarnin kotun jihar Kano da ya hana ‘yan sanda kama ko razana Rimin Gado, amma duk da haka aka take shi.

Source: Facebook
Abin da gwamnatin jihar Kano ta bukata
A ƙarshe, gwamnatin Kano ta bukaci a bi doka da kundin tsarin mulki wajen magance lamarin, sannan ta nemi a fadi hujjar kama Rimin Gado da kuma dalilin kai shi Abuja.

Kara karanta wannan
Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano
Sannan ta yi kira da a guji amfani da hukumomin tsaro wajen cimma muradun siyasa tare da tabbatar da kare haƙƙin ɗan ƙasa da mutunta 'yancin zuwa kotu.
Gwamnatin Kano ta yi wa Tinubu bayani
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta ƙara tsaurara dabarun tsaro a yankunan da ake kallon suna da rauni, domin dakile barna da dawo da zaman lafiya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya je ya yi wa shugaban kasa bayani kan yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa musamman a kan iyakar Kano da Katsina.
Abba ya nanata cewa gwamnatinsa ba za ta bar ko wane yanki ba tare da kariya daga ayyukan bata-garin mutane ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

