"Akwai Abin da ba a Karya da Shi": Rarara Ya Fadi Dalilin Aikin Alheri a Kauyensu

"Akwai Abin da ba a Karya da Shi": Rarara Ya Fadi Dalilin Aikin Alheri a Kauyensu

  • Fitaccen mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya ce ba kowane aikin alheri da mutum ya yi ne ake karya da shi ba
  • Ya bayyana haka ne bayan bude wani babban masallaci a kauyensa, inda ya wajibi ne duk wanda ke da iko ya tallafa wa inda ya fito
  • Mawakin ya shawarci masu abin hannu su rika taimaka wa jama’a ba tare da jiran gwamnati ba, musamman idan aikin da za su iya da aljihunsu ne

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahuta Rarara, ya bayyana manyan dalilan da suka sa ya ke gudanar da ayyukan alheri ga mutanen garinsa.

Rarara haifaffen kauyen Kahutu ne da ke jihar Katsina inda ya ke sama wa mutanen yankinsa abubuwan more rayuwa.

Kara karanta wannan

Albishir da ministan tsaro ya fara yi ga 'yan Najeriya bayan shiga ofis a Abuja

Dauda Kahutu Rarara ya fadi dalilan taimakon mutanensa
Mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Source: Twitter

A yayin da yake zantawa da RFI Hausa bayan bude sabon katafaren masallaci da ya gina, Rarara ya ce aikinsa na alheri ya samo asali ne daga son kyautatawa mahaifarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rarara ya fadi dalilin taimakon mahaifarsa

Mawaki Rarara ya bayyana cewa ya taso ne cikin mabukata, kuma wannan ya zame masa babban darasi da ba zai taba mantawa da shi ba.

A cewarsa:

“Babana almajiri ne, ni almajiri ne, iyayena ba masu karfi ba ne suka taso. Saboda haka, ba ni da wani wuri da ya fi wannan. Idan ba ka waiwaya baya ka ga inda ka fito ba, ba za ka gode wa Allah ba.”

Rarara ya ce yana ganin ya kamata ya rika godewa ga ni’imar da Allah ta hanyar tallafawa yankin da ya fito da abubuwna da za su saukaka masu.

Rarara ya shawarci masu abin hannu su rika taimako
Taswirar Jihar Katsina, mahaifar Dauda Kahutu Rarara Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cewarsa, ba wai kawai wani nauyi ne ba, har ma wata hanya ce da za ta tunatar da sauran masu iko cewa su ma su yi irin wannan aikin.

Kara karanta wannan

'Abin da ka shuka': Kotu ta yanke wa matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya

Ya ce:

“Ina yin shi a matsayin nuni ko tunatarwa ga duk wanda yake da dama. Ko kana Abuja, ko Legas, ko kasar waje, idan da damar da za ka taimaka wa mutanenka, hakki ne a kanka.”

Shawarwarin Dauda Rarara ga masu kudi

Rarara, wanda ya shahara a fagen wakar siyasa ya yi kira ga masu abin hannu su daina dogaro da gwamnati kan dukkannin bukatun al’umma.

Mawakin ya bayyana cewa akwai ayyukan da ba sai gwamnati ba, kamar samar da ruwan sha, cibiyoyin lafiya da sauran ayyukan jin kai.

Ya ce jerin ayyukan da ake bukata a kananan yankuna sun yi yawa, kuma idan an jira gwamnati ta yi su duka, lokaci zai iya ja al’umma na ci gaba da wahala.

A kalamansa:

“Akwai abu da ka san ya na kan shugaban kasa ne. Idan ya fi karfinka, sai ka zurawa saurautar Allah ido ko kuma ka yi wa gwamnati ta taimaka.”

Kara karanta wannan

Bwala: 'Yadda mahaifiyar Tinubu ta taka rawa a nadin manyan mukaman gwamnati'

Ya kuma jaddada cewa maganganun da wasu ke yi na cewa aikinsa yana da wata manufa ba su da tushe. A cewarsa, aikace-aikacen sa kamar gina masallatai ba ya daga cikin abubuwan da za a yi karya da su.

Rarara ya samu digirin girmamawa

A wani labarin, kun ji cewa mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara, ya yi martani bayan wata jami'ar Amurka ta girmama shi da digirin Dakta a ranar Asabar 20 ga watan Satumbar 2025.

Mawakin ya yi godiya ga jami’ar da ta ba shi wannan lambar yabo da kuma manyan jami’an da suka halarci bikin duk da cece-kuce da lamarin ya jawo musamman a shafukan sada zumunta a Arewacin Najeriya.

Ya tabbatar da cewa ko sisin kwabo bai biya ba, sabanin zargin da wasu ke yi, inda ya ce an karrama shi ne kawai saboda tasirinsa a duniyar mawakan siyasa da gudunmawar da ya ke bayarwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng