Gwamnoni 2 Sun Ajiye Banbancin Siyasa, Sun Kafa Rundunar Yaki da Yan Bindiga

Gwamnoni 2 Sun Ajiye Banbancin Siyasa, Sun Kafa Rundunar Yaki da Yan Bindiga

  • Gwamnonin jihohin Abia da Imo sun sha alwashin magance hare-haren da ake kai wa kan babban titin Aba zuwa Owerri a lokutan kirismeti
  • Gwamna Alex Otti da Hope Uzodinma sun kafa rundunar hadin gwiwa da ta kunshi sojoji da 'yan sanda domin tabbatar da tsaro
  • Rundunar za ta fara aiki daga ranar 5 ga watan Disamba, 2025 kuma za ta zafafa sintiri a dazuzzukan da ke gefen titin da ya hada Imo da Abia

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia, Nigeria - Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ta takwaransa na jihar Imo, Hope Uzodinma sun jingine banbancin siyasa domin kawo karshen hare-haren 'yan bindiga.

Gwamnonin biyu sun hada kai, sun kafa rundunar tsaron hadin gwiwa domin magance yawaitar hare-haren da ake fuskanta a kan babbar hanyar da ke haɗa jihohin biyu.

Kara karanta wannan

Malaman majami'u sun taru a Abuja, sun fito da gaskiya kan zargin kisan kiristoci a Najeriya

Gwamna Otti da Hope Uzodinma.
Gwamna Alex Otti na jihar Abia tare da takwaransa na Imo, Hope Uzodinma Hoto: Hope Uzodinma
Source: Facebook

Mai magana da yawun Gwamna Otti, Ferdinand Ekeoma, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a jiya Alhamis, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin biyu sun dauki wannan mataki ne a wani taron tsaro da suka yi a Owerri, mako guda bayan da ‘yan bindiga suka kai hari kan jami’ai uku na gwamnatin Abia a Owerri, babban birnin Imo.

Jihar Abia da Imo dai suna da iyaka mai tsawo, tare da yawan zirga-zirgar mutane da motoci a kan babban titin da ya hada jihohin biyu a Kudu maso Gabashin Najeriya.

Ayyukan da rundunar tsaron za ta yi

A cewar Ekeoma, rundunar hadin gwiwar za ta mayar da hankali ne kan sintiri a kan titin Aba zuwa Owerri, bibiya da sintiri cikin dazuzzuka da ke hannun dama da hagu na hanyar.

Kakakin gwamnan Abia ya kara da cewa rundunar za ta dakile ayyukan ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da sauran miyagun laifuka musamman yayin bukukuwan kirismeti a karshen shekara.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano

Ya ce rundunar za ta ƙunshi dakarun sojoji, ‘yan sanda, jami'an DSS da sauran jami’an tsaro, kamar yadda jaridar Vanguard ta kawo.

"Wannan rundunar tsaron hadin gwiwa za ta fara aiki daga ranar 5 ga Disamba 2025, kuma za ta yi sintiri a kan titin awanni 24 ba tare da tsayawa ba."
"Za ta gudanar da sintiri a cikin dazuzzukan da ke kewaye ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka da sauran kayan aikin tsaro na zamani," in ji Mista Ekeoma.

Gwamnoni 2 sun gargadi 'yan bindiga

A lokacin taron, Otti da Uzodimma sun tabbatar wa matafiya, musamman masu dawowa gida domin Kirsimeti, cewa za su kasance cikin tsaro a dukkan yankin hanyar.

Sun gargadi miyagu da duk masu hannu a kai hare-haren kan titin cewa hukunci mai tsanani zai biyo baya idan aka cafke su.

Gwamna Alex Otti.
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti yana jawabi a fadar gwamnatinsa Hoto: Alex C. Otti
Source: Facebook

Gwamna Otti ya yaba wa Uzodimma kan damke wadanda suka kai hari ga jami’an gwamnatin Abia a Owerri, yana mai cewa hakan ya nuna jajircewar gwamnatin Imo wajen yaki da miyagun laifuka.

Gwamna Otti ya ziyarci Nnamdi Kanu

Kara karanta wannan

Wasu manyan matsaloli 5 da Janar Musa zai fuskanta idan ya zama ministan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Abia Alex Otti ya kai ziyarar farko ga Nnamdi Kanu a gidan gyaran hali da ke Sakkwato bayan hukuncin daurin rai da rai.

A wannan ziyara, Gwamna Otti ya tabbatar da cewa alkawarin da ya dauka na kokarin ganin an sake Nnamdi Kanu na nan daram.

Aloy Ejimakor, tsohon lauyan Nnamdi Kanu, ya jinjinawa Otti bisa wannan ziyara, inda ya bayyana fatan zai zamo alheri ga shugaban IPOB.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262