Kuɗin da Yawa: Gwamna Zulum Ya Faɗi Biliyoyin Naira da Ya Kashe kan Tsaro a 2025
- Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kashe N100bn a ayyukan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a
- Zulum ya bayyana hakan ne a ziyarar da ya kai wa Sarkin Uba, inda ya je duba matsalolin tsaro da suka hana ci gaban ayyukan gine-gine
- Ya bayyana shirinsa na gina makarantu, cibiyar kwamfuta, cibiyar JAMB, hanyoyi da kuma kafa jami’a domin inganta rayuwar Askira/Uba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kashe kusan N100bn wajen samar da tsaro a jihar cikin shekarar 2025.
Babagana Zulum wanda zai bar mulki a watan Mayun 2027 ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ban-girma ga sarkin masarautar Uba, Alhaji Ali Ibn Mamza.

Source: Twitter
Gwamna Zulum ya yi magana kan rashin tsaro
Mai girma gwamna ya ce ya ziyarci masarautar ne domin jajantawa sarkin da al'ummarsa kan hare-haren baya-bayannan da suka yi sanadin rasa rayuka, in ji rahoton Daily Trust.
Zulum ya yi ta’aziyya ga masarautar Uba bisa rasa rayukan da aka yi a harin da 'yan bindiga suka kai yankin, yana mai yabawa jami’an tsaro kan ceto mata 12 da aka yi garkuwa da su.
Gwamnan ya ce ya kawo ziyarar ne domin gane wa idanunsa ainihin matsalolin tsaron da ke hana cigaba a Askira/Uba tare da nemo hanyoyin magance su.
Zulum ya yi magana kan yadda matsalolin tsaro ke tsoratar da ‘yan kwangila, lamarin da ya jawo tsaiko a manyan ayyuka, musamman ginin hanyoyi da gyaran manyan gine-gine a yankin.
"Na kashe N100bn a kan tsaro' - Zulum
Saboda wannan dalili, Zulum ya fadawa sarkin cewa gwamnati ta kafa masana'antar fasa dutse a Gwoza tare da sayen manyan motocin daukar kaya 100, domin gyara da gina hanyoyi da kanta.

Kara karanta wannan
Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano
Zulum ya sake tabbatar da alkawarin da ya dauka na gina jami’a ko manyan makarantu a yankin kafin ya kammala wa’adinsa, in ji rahoton Daily Post.
Ya ce ya zuwa yanzu, ya shirya gina cibiyar koyar da kwamfuta, cibiyar rubuta jarabawar JAMB, asibitoci, da hanyoyi domin bunkasa yankin.
Ya kara da cewa:
“A wannan shekara kawai, abin da na kashe a kan tsaro ya kai kusan N100bn. Muna da shirye-shirye a fannin ilimi da lafiya, kuma mun kashe kudi sosai wajen samar da abubuwan more rayuwa.”

Source: Original
Sarkin Uba ya yabawa Gwamna Zulum
A jawabinsa, Sarkin Uba, Alhaji Ali Ibn Mamza, ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Zulum bisa ware lokaci ya ziyarci masarautar a irin wannan lokaci na bakin ciki.
“Ka yi mana ayyuka masu yawa, kuma ka yi alkawari za ka kara. Da ba don saboda kokarinka ba, da mun shiga mawuyacin hali. Da za a iya gyara kundin tsarin mulki, da mun roki ka ci gaba da mulki.”
- Alhaji Ali Ibn Mamza.
Zulum ya mika bukata ga rundunar sojoji
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya mika kokon bararsa ga rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) kan mayakan Boko Haram da ISWAP.
Gwamna Zulum ya bukaci rundunar da ta tura jiragen yaki domin kawar da 'yan ta'addan daga yankunan tafkin Chadi, dajin Sambisa, Timbuktu Triangle da tsaunukan Mandara.
Ya kuma yaba da tura jirage marasa matuƙi da sauran kayan aiki, tare da yin alkawarin bada cikakken goyon bayan gwamnatin jihar domin tabbatar da nasarar ayyukan jami'an tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

