'Abin da Ka Shuka': Kotu Ta Yanke wa Matashi Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya
- Kotu a Maiduguri ta yanke wa makiyayi mai shekara 18 hukuncin kisa ta rataya bayan tabbatar da laifin kashe wani saurayi
- Alkalin kotu ya bayyana cewa kisan ba wai kare kai ba ne, domin babu abin da ya nuna cewa matashin ba zai iya gudu wa daga rikicin ba
- Wanda ake tuhuma, Adamu Mohammed ya amince cewa ya yi fada da mamacin da adda, kuma ya sara masa a lokacin da rikici ya kaure a tsakaninsu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kotun babban birnin Maiduguri ta yanke wa wani matashin makiyayi mai suna Adamu Mohammed, mai shekara 18, hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta tabbatar da laifin kashe wani abokin kiwonsa, Adamu Ali, wanda shi ma matashi ne mai shekara 19.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a Auno, karamar hukumar Konduga a jihar Borno, yayin da su biyun suka fara rigima a cikin daji a ranar 19 ga Janairu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta kama Bafulatani da laifi
Daily Post ta ruwaito cewa bayanan kotu sun nuna cewa duk da cewa Mohammed ya amsa laifin lokacin da aka kama shi, kotu ta shigar masa da shaidar bai amsa zargin ba saboda lafiin na dauke da hukuncin kisa.
A zaman shari’ar, masu gabatar da ƙara sun kawo shaidu biyu tare da gabatar da bayanan da wanda ake tuhuma ya bayar a wajen ‘yan sanda da kuma rahoton likita.
A cikin bayanansa biyu, Mohammed ya amince cewa ya yi fada da mamacin da adda, kuma ya sara masa a lokacin da rikici ya kaure a tsakaninsu.

Source: Facebook
Sai dai lauyansa ya yi ƙoƙarin kare shi da hujjar cewa ya yi hakan ne domin ya kare kansa. Amma kotu ta yi watsi da wannan, tana mai cewa an samu baki biyu a kan lamarin.
Kotu ta kara da cewa babu wata shaida da ke cewa wanda ya yi kisan ba shi da wata hanya ta gudu ko tsira ba tare da kai wannan bugun da ya zama sanadiyyar mutuwar abokinsa ba.
Kotu ta yankewa Bafulatani hukuncin kisa
Mai shari’a Maina ya bayyana cewa karfin da wanda ake tuhuma ya yi amfani da shi ya zarce misali, saboda haka ba ya shiga kariyar da doka ta tanada.
Ya ce abin da ya aikata ya cika dukkannin sharuɗɗan kisan kai a ƙarƙashin Sashe na 191(a) na Dokar Penal Code ta Jihar Borno, 2023.
Daga ƙarshe, kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, kamar yadda dokar jihar ta tanada.
Kotu ta yankewa dalibi hukuncin kisa
A baya, mun wallafa cewa wata babbar kotu a Jihar Ribas ta yanke wa wani ɗalibi, Damian Okoligwe, hukuncin kisa ta hanyar rataya, wanda ya kawo karshen zargin kisan kai da ake yi masa.
Kotun ta tabbatar da cewa an gabatar da hujjoji da suka nuna cewa Damian ya kashe masoyiyarsa, Justina Otuene, kuma an tabbatar da cewa ya aikata wannan mugun laifi ne a cikin hayyacinsa.
Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 20 ga Oktoba, 2023, a sabon gidan dalibin jami'ar da ke Mgbuoba, karamar hukumar Obio/Akpor, inda matashin ya yi gunduwa gunduwa da Justina.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


