Lamari Ya Girma: ’Yan Fansho Za Su Fito Tsirara yayin Zanga Zanga a Najeriya

Lamari Ya Girma: ’Yan Fansho Za Su Fito Tsirara yayin Zanga Zanga a Najeriya

  • Kungiyar yan fansho a Najeriya sun shirya gudanar da zanga-zanga na musamman domin neman hakkinsu
  • Tsofaffin ma’aikatan gwamnatin tarayya sun sanar da shirin gudanar da zanga-zangar tsirara a fadin kasa
  • Shugaban kungiyar ya bayyana damuwa kan basukan da suke bi inda ya fadi lokaci da ranar da za su zanga-zanga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar Tsofaffin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta bayyana cewa tana shirin gudanar da zanga-zanga a fadin kasa baki daya.

Kungiyar ta ce za ta yi zanga-zangar tsirara a fadin kasar domin neman a biya su basussukan da suke bin gwamnati wanda ya dauki lokaci mai tsawo.

Yan Fansho sun yi argadi ga gwamnatin Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Yan fansho za su fito zanga-zanga tsirara

Shugaban ƙungiyar na kasa, Mukaila Ogunbote, wanda kuma shi ne shugaban NUP reshen NIPOST, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: NLC na shirin zazzafar zanga zanga a dukkan jihohin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ogunbote ya ce za a gudanar da zanga-zangar saboda bashin karin kudin fansho da kuma tallafin da aka amince da su tun 2023.

Ya ce zanga-zangar za ta gudana ne a ranar 8 ga Disambar 2025, sai dai idan gwamnatin tarayya ta biya su ragowar N32,000 na karin fansho da kuma N25,000 na tallafin watanni shida kafin lokacin.

Fansho: Zargin da ake yi wa gwamnatin tarayya

Ogunbote ya zargi Ma’aikatar Kudi ta Tarayya da Ofishin Akanta Janar da rashin daukar su da muhimmanci, cewar The Guardian.

Ya kuma tabbatar da cewa lokaci ya yi da dukkan tsofaffin ma’aikata za su fito su nemi hakkokinsu cikin hadin kai.

Daga bisani, ya ce zanga-zangar za ta gudana ne a Abuja, Lagos da sauran jihohi, musamman a gaban ofisoshin PTAD da kuma gidajen talabijin na NTA.

Za a gudanar da zanga-zanga tsirara a Abuja
Taswirar birnin tarayyar Najeriya da ake kira Abuja. Hoto: Legit.
Source: Original

Rokon da aka yi ga mambobin kungiyar

Har ila yau, ya bukaci shugabanni da sakatarorin dukkan kungiyoyin da ke karkashin hadakar su tattara yan fansho domin fitowa kwansu da kwarkwata.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano

Ya kara da cewa:

“Dole mu fito mu nuna irin ciwon da tufafinmu ke boyewa, zanga-zangar ba za ta tsaya ba sai mun karɓi sakon shigar kudin N32,000 da N25,000 har na wata shida.
"Wadanda za su zo ba za su koma ba su taho da tabarma domin kasancewa na tsawon lokaci."

- Mukaila Ogunbote

Ogunbote ya jaddada cewa lokaci ya yi da dukkan tsofaffin ma’aikata za su tashi tsaye su kare hakkinsu domin tabbatar da ceto rayuwarsu daga masu neman kassara su.

Yan Fansho sun gargadi gwamnatin Tinubu

A baya, mun ba ku labarin cewa tsofaffin ma’aikatan gwamnatin tarayya sun yi barazanar gudanar da zanga-zangar tsirara a fadin kasar nan a ranar 6 ga Oktobar shekarar 2025.

Sun ce har yanzu ba su samu kudaden tallafin N25,000 da karin fansho ba, duk da umarnin shugaban kasa Bola Tinubu.

Ma'aikatan sun koka da cewa ma’aikata na samun tallafi da karin albashi, amma tsofaffin ma’aikata na cikin halin kunci da fatara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.