Sulhu da 'Yan bindiga: Sheikh Gumi Ya Yi wa Ministan Tsaro, Janar Musa Martani
- Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce babu wani lokaci da ya taɓa goyon bayan ’yan bindiga, yana mai cewa addini bai yarda da zalunci ba
- Ya yaba wa sabon ministan tsaro Janar CG Musa (mai ritaya) kan matsayinsa na cewa ba zai yi sasanci da miyagun ’yan bindiga ba
- Malamin ya ce ya nemi a yi wa Nnamdi Kanu afuwa ne idan zai tuba, kamar yadda aka yi wa Chukwu Ojukwu da ’yan Neja Delta a baya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya sake fayyace matsayinsa kan matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan.
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana yana mai cewa ba ya goyon bayan duk wani tsari da zai bai wa ’yan bindiga damar ci gaba da aikata ta’addanci.

Source: Facebook
Malamin ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC Hausa, inda ya yi karin bayani game da dalilan da ya sa ya goyi bayan sulhu da 'yan bindiga.
Sheikh Gumi ya ce akasin abin da wasu ke zato, aikinsa ba ya goyon bayan 'yan ta'adda, sai dai ƙoƙarin wajabta gaskiya da sanar da wadannan mutane haramcin abin da suke yi.
Matsayar Ahmad Gumi kan bayanin sabon ministan tsaro
Sheikh Gumi ya yi tsokaci kan kalaman sabon ministan tsaron Najeriya, Janar CG Musa (mai ritaya), wanda ya ce babu sasanci da ’yan bindiga.
Malamin ya bayyana cewa wannan matsaya ta yi daidai da tsarin da ya dace da aikin soja, domin ya nuna ƙarfin gwamnati da ƙudirinta na kawo ƙarshen ta’addanci.
Ya ce soja ba ya sassauci domin shi ne tubalin ƙarfi a tsarin tsaro, kuma bai kamata soja ya nuna rauni ga ’yan ta’adda ba.
Malamin ya jaddada cewa kodayake sau da yawa yana magana kan sulhu, hakan ba yana nufin sassauci ba ne, sai dai domin neman mafita.
Ya kara da cewa maganar minstan tsaro ba za ta hana gwamnati tattaunawa da 'yan bindiga ba idan ta ga haka ne mafita mafi dacewa.
Batun neman afuwa ga Nnamdi Kanu
A bangare guda, Sheikh Gumi ya tabo batun Nnamdi Kanu, jagoran haramtacciyar ƙungiyar ’yan a-ware ta IPOB, wanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samunsa da laifin ta’addanci.
Ya ce neman afuwar da ya yi ba wai don goyon baya ba ne, sai dai don ganin an samu zaman lafiya kamar yadda aka taba cimmawa a tarihin Najeriya.

Source: Twitter
Malamin ya ce idan har Kanu zai amince da nadama, ya tuba, sannan ya umarci magoya bayansa su ajiye makamai, to zai nemi a yi masa afuwa kamar yadda gwamnati ta aiwatar ga wasu a baya.
Ya yi nuni da yadda shugaba Shehu Shagari ya yi wa Chukwuemeka Ojukwu afuwa bayan yakin basasa da ya yi sanadin mutuwar sama da miliyan biyu.
Ya kara buga misali da yadda shugaba Umaru Musa Yar’Adua ya yi wa ’yan Neja Delta afuwa a lokacin tashin hankalin yankin.
Gumi ya daina shiga daji wajen 'yan bindiga
A wani labarin, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya ce ya daina shiga daji sulhu da 'yan bindiga.
Yayin da ya ke hira da manema labarai, Sheikh Gumi ya ce tun lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari bai sake shiga daji ba.
Malamin ya bayyana cewa ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda ne ya sanya shi daina shiga wurarensu a dazukan Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


