'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane saboda 'Rufaida Yoghurt' a Zamfara
- Ƴan bindiga sun kai hari a Danjibga da ke jihar Zamfara bayan takaddama saboda 'yoghurt' dan N3,500
- Wannan lamari ya yi zafi, bar an kashe mutane uku, yayin da ƴan ta'addan suka riƙa ɓalla shagunan jama'a
- Mutane sun yi martani mai zafi a shafukan sada zumunta, suna tambayar me gwamnati ke yi ake wannan aiki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Mummunan rikici a kan madarar 'Rufaida Yoghurt' ya salwantar da rayukan bayin Allah da jawo sace-sace a jihar Zamfara.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru a daren jiya a ƙauyen Danjibga da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, inda aka kwana ana fargaba.

Source: Original
Bakatsine ya wallafa shafinsa na X cewa wasu ƴan bindiga sun shiga wani shago suka nemi su tafi da 'Rufaida Yoghurt' na kimanin N3,500 ba tare da sun biya ba.
Rikici ya ɓarke a jihar Zamfara
Rahoton ya ce da mutanen suka so daukar madarar, sai Mai shagon ya nace dole a biya kafin a tafi, hakan ya fusata su, suka bar madarar, suka fita.

Source: Facebook
Bayan ƙasa da sa’a guda, suka dawo dauke da bindigu suka fara harbe-harbe, lamarin da ya janyo mutuwar mutane uku, ya sa mazauna yankin su gudu, sannan suka yi fashin shagon.
Rahoton ya ce jama'a na cikin fargaba a Zamfara, domin ƙungiyoyin ƴan bindiga na yawo daga wuri zuwa wuri suna abin da suka ga dama.
An yi tir da harin 'yan bindiga a Zamfara
Jama'a da dama ne suka yi martani a kan wannan mummunan al'amari, wanda ya sa suka nemi jin yadda gwamnati ta Gaza a fannin tsaro.
@Voix_of_d_north – 18h ya ce:
“Ana kashe su saboda madara, amma wasu marasa hankali suna yi mana wa’azin sasanci da waɗannan halittu masu shan jini. Wannan hauka ne. Wallahi Arewa muna cikin mummunan hali.”
@Im_KiNg_PhArAoH ya ce:
“’Yan ta’adda Fulani sun zama kamar sarakunan ƙasar Hausawa da aka cinye.”
@IliyaBenoni ya kara da cewa:
“Me gwamna yake yi akai?”
@cale_fischer
“Allahu Ya tsare Najeriya. Yanzu kamar ƴan bindiga suna da iko a Zamfara, Sokoto da Katsina domin labaran da ke fitowa daga can suna tayar da hankali.”
@OlanusiAkin
"Wadannan abubuwa suna faruwa kullum a Najeriya ba a Mali ba, kuma jami’an tsaro kamar ba su da halin yin komai. Akwai wani abu da ya ɓace.”
@TakkeProfits “Nawao! Saboda 'yoghurt' na ₦3,500 ka kashe ɗan Adam? Dabbobi!”
@dieslunae10
“Wannan ‘fim’ ɗin da shugabannin Arewa suka tsara, ka tabbata za su iya kammala shi? Yaya mutum zai haddasa barna saboda yoghurt?”
An cafke hatsabibin ɗan ta'adda a Zamfara
A baya, mun wallafa cewa rundunar ‘yan sanda ta musamman, watau Scorpion Squad, ta yi nasarar kama wani fitaccen ƙungiyar masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara.
An gano cewa waɗanda aka kama su ne Dalhatu Bashiru da Chidiebere Nwadigo Emmanuel mai shekaru 34 da ake nema ruwa a jallo bisa zargin hana bayin Allah sakat.
Rahotanni sun ce dukkanninsu tsofaffin fursunoni ne, kuma suna daga cikin jerin masu laifi da ake nema kan garkuwa da mutane da satar motoci da sauran miyagun ayyuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


