Sheikh Gumi Ya Yi Zazzafar Addu'a kan 'Yan Ta'adda da Masu Taimakonsu

Sheikh Gumi Ya Yi Zazzafar Addu'a kan 'Yan Ta'adda da Masu Taimakonsu

  • Ahmad Gumi ya fitar da addu’a mai zafi yana neman Allah ya fallasa tare da hukunta duk wanda ke da hannu ko amfana da tashin hankali a Najeriya
  • Masu amfani da kafar sada zumunta sun yi martani, wasu na goyon baya, wasu na suka, inda Gumi ke mayar da martani da kalmar neman a ce 'Amin'
  • Addu'ar Sheikh Gumi na zuwa ne yayin da Najeriya ke fama da hare-haren 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya sake magana kan matsalar tsaron Najeriya, inda ya yi addu’a mai zafi.

A cikin wannan addu’a, Dr Ahmad Gumi ya roƙi Allah Madaukakin Sarki ya tona asirin duk wanda ya ke tallafawa rashin tsaro da jinin da ake zubarwa a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Bello Matawalle ya samu kariya ana tsaka da kiran Tinubu ya kore shi

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Sheikh Ahmad Gumi yayin wani wa'azi da ya yi. Hoto: Salisu Hassan Webmaster
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a Facebook mai taken 'Addu’ata a yau,' malamin ya roƙi Allah ya yi maganin duk wanda ke da hannu kai tsaye ko ta bayan fage wajen haifar da rashin tsaro.

Sakon ya haifar da muhawara a shafinsa, inda wasu mabiyansa suka yi amanna da addu’ar, wasu kuma suka yi suka, inda shi kuma Gumi ke bayar da amsa ta hanyar faɗin a ce “Amin.”

Addu’ar Ahmad Gumi da martanin jama’a

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa a cikin sakon zazzafar addu’ar da ya wallafa, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi roƙon cewa:

"Ya Allah! Duk wanda ya kirkiro rashin tsaro ko ya ke goyon bayan zubar da jini a Najeriya, dan kasar wajen ne ko ɗan Najeriya, ko ya ke amfana da shi, ko yana farin ciki da kashe-kashe, ko ya ki daukar mataki domin dakatar da shi kuma yana da dama, ka tona asirinsa kuma ka daura masa fushinka cikin gaggawa ba tare da cutar da marasa laifi ba. Amin."

Kara karanta wannan

An kama wasu 'yan kasashen waje da suka shigo Najeriya ta'addanci

Daya daga cikin masu martani, Sani Badamasi, ya rubuta cewa kalaman da ake yi na sulhu da ’yan bindiga na iya ƙara musu kwarin gwiwa fiye da makami.

A cewarsa, akwai maganganu da su kansu sun fi daukar makami hatsari. Gumi ya amsa masa da cewa:

"Ka ce Amin kawai."

Wani mai suna, Endless Joe, ya rubuta cewa duk wanda ya taɓa tallafawa 'yan ta'adda Allah ya sa kar ya kai karshen 2025, sai Gumi ya amsa da cewa:

"Amin ga dukkan makiyan Najeriya, har da ’yan bindiga. To ku ce Amin ga addu’ata ma!"
Sheikh Gumi da shugaba Bola Tinubu
Sheikh Ahmad Gumi da Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Salisu Hassan Webmaster
Source: Facebook

'An daina sulhu da 'yan bindiga,' CG Musa

A wani labarin, kun ji cewa sabon Ministan tsaro ya bayyana cewa daga lokacin da ya fara aiki ba za a sake sulhu da mika kudin fansa ga 'yan bindiga ba.

Janar Christopher Musa (Mai ritaya) ya bayyana haka ne yayin da majalisar dattawan Najeriya ke tantance shi a ranar Larabar da ta wuce.

Daga cikin hujjojin da ya kawo ya ce kudin fansa da ake ba 'yan ta'adda na taimaka musu wajen samun damar sayen makamai su cigaba da kai hari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng