‘Ina cikin Aminci a Najeriya’: Tsohon Firayim Ministan Burtaniya kan Tsaro

‘Ina cikin Aminci a Najeriya’: Tsohon Firayim Ministan Burtaniya kan Tsaro

  • Tsohon Firayim Ministan Biritaniya, Boris Johnson, ya yi magana game da yada matsalolin tsaro a Najeriya
  • Johnson ya ce ya ji cikakkiyar tsaro a Owerri duk da rahotannin tsaro da suka gabace shi kafin zuwansa Imo
  • Ya yaba wa Gwamna Uzodimma kan kokarin samar da wutar lantarki na awa 24, yana cewa gwamnan na ba da gudunmawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Owerri, Imo - Tsohon Firayim Ministan Biritaniya, Boris Johnson, ya bayyana cewa ya ji cikakkiyar kariya da tsaro yayin ziyarar da ya kai Najeriya.

Johnson ya fadi haka ne duk da rahotannin tabarbarewar tsaro da suka gabaci tafiyarsa zuwa Owerri, babban birnin Imo.

Tsohon firayim minista ya maganti kan tsaro a Najeriya
Tsohon fitayim ministan Burtaniya, Boris Johnson. Hoto: Boris Johnson.
Source: Facebook

Johnson ya magantu kan rashin tsaron Najeriya

Johnson ya yi wannan jawabi ne a wajen taron tattalin arziki a Imo ta shekarar 2025 wanda Gwamna Hope Uzodimma ya shirya, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Janar Christopher Musa ya sha sabon alwashi bayan zama Ministan tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Johnson ya ce lokacin da ya yanke shawarar zuwa Owerri an yi ta yi masa magana da tamayar shi bai ganin abubuwan da suke faruwa.

Ya ce amma ko kadan maganganun ba su yi tasiri ba, ya yi kokari ya zo duk da haka domin halartar taron.

Ya ce:

“Lokacin da na yanke shawarar zuwa Owerri, na karanta wasu rahotanni da ke cewa ‘akwai matsalar tsaro a Najeriya, amma na ce zan zo duk da haka. Kuma ku gaya min: kuna jin tsaro a nan? Ni ma haka, na ji cikakkiyar tsaro. Na gode, Gwamna.”
Boris Johnson ya shiga Najeriya duk da matsalar tsaro
Tsohon fitayim ministan Burtaniya, Boris Johnson. Hoto: Boris Johnson.
Source: UGC

Johnson ya yabawa Gwamna Uzodinma

Johnson ya kuma yaba wa gwamnan bisa yunkurinsa na samar da wutar lantarki awa 24, yana mai cewa fasahar AI zai taka muhimmiyar rawa.

Ya ce:

“Burinka na wutar lantarki ya dace. Makomar duniya ita ce AI. Saboda AI, wutar lantarki mai tsafta da dorewa za ta zama babbar dama.”

Kara karanta wannan

Ministan tsaro, Janar Musa ya ware gwamnoni 6 da suka yi fice a kokarin samar da tsaro

Ya kara bayyana cewa dangantaka tsakanin Najeriya da Biritaniya tana da dadadden tarihi, tare da musayar kwararru da ma’aikata masu basira, cewar Channels TV.

A kalamansa:

“Muna turo muku magunguna, bankuna da kayan motoci. Ku kuma kuna turo mana da man fetur, Nollywood, kwararrun likitoci, nas da masu fasaha. Har ma kuna turo mana shugabannin gwamnati irinsu Kemi Badenoch.”

Taron ya samu halartar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu; tsohon sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon; attajiri Aliko Dangote; ministan kudi Wale Edun; da wasu gwamnoni.

Jawabin Johnson dai ya zo ne a lokacin da Najeriya ke fama da sababbin tashe-tashen hankula na matsalolin tsaro, ciki har da sace mutane da dama a jihohi daban-daban.

Lamura suka kara daukar hankali bayan shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki gwamnatin Najeriya kan gazawa kare al’ummomin Kiristoci.

Gwamna ya koyawa dubban matasa sana'o'i

A baya, an ji cewa Gwamna Hope Uzodinma ya tuna da matasa a Imo bayan Bola Tinubu ya ziyarci jihar domin kaddamar da ayyuka.

Kara karanta wannan

A karshe, majalisa ta amince da nadin Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaro

Uzodinma ya horar da matasa 50,000 a jihar ta hanyar shirin 'SkillUp' Imo domin ba su ƙwarewar zamani da inganta rayuwarsu.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yaba da shirin, yana cewa Gwamnan ya farfaɗo da kwarin guiwar matasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.