Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai yi murabus daga shugabancin jam’iyyar sa

Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai yi murabus daga shugabancin jam’iyyar sa

  • Ana san ran Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai sauka daga mukamin na shugaban jam'iyar conservatives a yammacin yau Alhamis
  • Duk da cewa Boris Johnson bai kammala yin murabus ɗin ba a hukumance, an fara kamfe kan wanda zai gaje shi.
  • Mista Johnson zai cigaba da zama firaministan kasar har zuwa watan Oktoba kafin a nada wanda zai maye gurbin sa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ingila - A Yau Alhamis ne Firaministan Birtaniya Mista, Boris Johnson zai sauka daga mukamin shugabancin jam’iyyar ta Conservatives. Rahoton BBC HAUSA

Mista Johnson zai cigaba da zama firaministan kasar har zuwa watan Oktoba.Yanzu za a nada sabon shuagaban jam’iyyar Conservative da zai maye gurbin sa, sannan a zabi sabon Firaminista a watan Oktoba

Har an fara yin kamfen din wanda zai gaji Boris duk da cewa bai kammala yin murabus din ba a hukumance.

Kara karanta wannan

Okupe: Abin da ya sa tun tuni Peter Obi ya yi watsi da maganar dunkulewa da Kwankwaso

BORIS
Firaministan Birtaniya Boris Johnson zai yi murabus daga shugabancin jam’iyyar sa ; FOTO REAUTERS
Asali: UGC

Firaminista Boris Johnson zai bayyana yin murabus din nasa ne zuwa anjima, yau ranar Alhamis

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai Magana da yawun fadar gidan gwamantin Ingila Mai Lamba 10 Darwin street ya ce: "Firaministan zai yi sanarwa ga ƴan ƙasar zuwa an ji ma."

Firaminista Boris Johnson ya yi magana ne da Sir Graham Brady, shugaban kwamitin jam'iyyar Conservative na 1922 , inda ya sanar da shi matakin da ya ɗauka, inji majiyar.

Majiyar ta ƙara da cewa: "Mista Boris Johnson ya yi magana da Graham Brady inda ya amince ya sauka a kan lokaci don ba da damar naɗa wani sabon shugaban a Oktoba."

Ma’aikata sun batar da fasfon Bayin Allah, maniyyata ba za su yi aikin Hajjin bana ba

Ghana - A kasar Ghana, an jefa masu niyyar yin aikin hajjin wannan shekara a tsaka mai wuya, domin an nemi takardunsu, duk an rasa.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya nesanta kansa da wani Hoto da aka ɗora shi kan daddumar Sallah

Wani labari mara dadi da ya fito daga VOA Hausa, ya bayyana cewa akalla maniyyata 176 ne aka rasa inda takardun fasfonsu suka shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel