Karancin Abinci: Manoma 14,000 Sun Samu Tallafin N4bn a Jihar Bauchi

Karancin Abinci: Manoma 14,000 Sun Samu Tallafin N4bn a Jihar Bauchi

  • Wata gidauniya ta taimakawa ƙananan manoma da wani tallafi domin inganta harkokin noma a Najeriya
  • Akalla ƙananan manoma 14,000 daga kananan hukumomi bakwai na Bauchi suka amfana da shirin na noman zamani
  • Shirin ya mayar da hankali kan horaswa, ingantattun kayayyakin noma domin ƙarfafa mata da matasa, tare da inganta ƙarfin samun kudin shiga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Wata gidauniya ta tallafawa kananan manoma a jihar Bauchi domin samar da abinci a jihar.

An ce akalla kananan manoma 14,000 ne a Bauchi suka ci gajiyar shirin noma na zamani a yanzu da duniya ta cigaba.

Manoma sun samu tallafin N4bn a Bauchi
Dandazon manoma a shirin samar da ingantaccen abinci a Bauchi. Hoto: Salisu Ibrahim.
Source: UGC

Kananan manoma sun samu tallafin N4bn

Daya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar wannan shiri, Samuel Luka shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa.

Kara karanta wannan

Wasu manyan matsaloli 5 da Janar Musa zai fuskanta idan ya zama ministan tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Luka wanda ya fito daga karamar hukumar Zaki ya ce tabbas sun ji dadin wannan tallafi musamman a wannan lokaci.

"Muna lale marhabun da wannan tallafi ganin cewa sun yi mana alkawarin taikama mana wurin sayar da kayan da aka noma cikin farashi mai kyau."

- Samuel Luka

Har ila yau, Luka ya ce taimakon ya zo a daidai duba da yadda aka samu sauyin yanayi a yankunansu.

Shugaban hulda da jama'a na kamfanin Nigeria Breweries, Chukwuemeka Aniukwu ya ce Gidauniyar Heineken Africa tare da hukumar NB ne saka hannun jari na Naira biliyan hudu saboda shirin.

Ya bayyana haka a taron kaddamar da shirin ƙarfafa kananan manoma domin jure canjin yanayi.

Ya ce zuba jari a Bauchi na nuna amincewa da ƙoƙarin manoma, saboda jajircewa da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen samar da abinci a Najeriya.

Aniukwu ya jaddada cewa shirin zai ba manoma, musamman mata da matasa, damar samun ƙwarewa, ingantattun kayan noma, da damar shiga kasuwa cikin daraja.

Kara karanta wannan

Shugaban gwamnonin Arewa ya ce sun ga uwar bari game da rashin tsaro

Manoma sun samu tallafin N4bn a Bauchi
Taswirar jihar Bauchi na daga cikin jihohi da ta rike harkar noma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Amfanin da manoman da zu samu

Daraktan FSSS, Dr Isaiah Gabriel, ya ce za a koyar da manoma ta tsarin 'Farmer Field' ta hanyar filayen gwaji domin samun horo kai tsaye.

Ya bayyana cewa cikin manoma 14,000, mata ne kaso 60, yayin da matasa suka kai kaso 40, domin ƙarfafa su shiga harkokin noma.

Shirin zai mayar da hankali kan noma da zai jure sauyin yanayi, kiyaye ƙasa da ruwa, sarrafa ƙwari, bambancin amfanin gona da ingantaccen kula bayan girbi.

FSSS ta ce shirin zai taimaka wajen farfaɗo da albarkatun ƙasa, rage barna, da samar da dabarun noma masu jure fari da inganta amfanin gona.

Gabriel ya ce burinsu shi ne ƙara kudin shiga manoma da akalla kashi 30, yana mai jaddada cewa mata da matasa suna tsakiyar wannan muhimmin shiri.

Kwamishinan noma na Bauchi, Iliyasu Gital, ya yabawa shirin tare da tabbatar da irin goyon bayan gwamnati domin tabbatar da nasarar horon manoma.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnati ta yi bayani kan dokar hana acaba, an yi sassauci a wasu yankuna

Gidauniya ta tallafawa dalibai a Bauchi

An ji cewa Gidauniyar Ibrahim Ali Usman ta raba fom na JAMB guda 300 ga dalibai da aka zaba daga yankin Bauchi ta Kudu.

Daliban makarantar sun fito daga kananan hukumomi bakwai, kuma an bi ka’ida wurin tantance wadanda suka fi cancanta.

An tabbatar da wanda ya ci jarabawar JAMB, Gidauniya za ta dauki nauyin karatunsa har zuwa jami’a ko kwalejin ilimi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.