Shari'ar Musulunci: MURIC Ta Kalubalanci Amurka, Ta Faɗi Abin da Musulmi Za Su Yi
- Kungiyar MURIC ta yi martani mai zafi game da neman a soke shari'ar Musulunci da kuma rusa Hisbah a Arewa
- MURIC ta nesanta kanta daga kiran wani masani a Amurka da ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta aiwatar da shawarar
- Farfesa Ishaq Akintola ya ce kiran ya sabawa doka, yana nuni da yunƙurin tauye ikon Najeriya da dokokinta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kungiyar Kare Hakkokin Musulmi MURIC ta kalubalanci Amurka kan batun soke shari'ar Musulunci.
Kungiyar ta yi watsi da kiran Dr Ebenezer Obadare, babban masani daga Amurka, da ya nemi shiga cikin harkokin Shari’ar Najeriya.

Source: Twitter
Hakan na cikin sanarwar da kungiyar ta wallafa a shafinta na yanar gizo wanda Legit Hausa ta gano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da Obadare ya ce kan shari'ar Musulunci

Kara karanta wannan
Hadimin Tinubu ya yi martani mai zafi kan kiran Amurka ta hana dokar shari'a a Najeriya
Ebenezer Obadare ya bukaci Amurka ta matsa wa Shugaba Bola Tinubu ya haramta Shari’a da hukumomin Hisbah, wani batu da MURIC ta ce ba za ta lamunta ba.
A sanarwar Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana kiran a matsayin wuce gona da iri, yana kuma sanya ayar tambaya da shakku kan manufar Amurka.
Ya ce kiran ya fito ne daga wani zaman Majalisar Amurka, bayan matakin Shugaba Donald Trump na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ke da babbar matsala.
Akintola ya yi gargadin cewa wannan matsin lamba na iya nuna Amurka ba ta da niyya mai kyau, yana ganin hakan tamkar mika ikon Najeriya ne ga waje.
Ya ce sukar Shari’a ya sabawa kundin tsarin mulki, kuma babu hakkin Amurka ko gwamnatin Najeriya ta tabo wannan fanni da al’ummar Musulmi suka amince da shi.

Source: Facebook
MURIC ta dura kan Obadare saboda Shari'ar Musulunci
Farfesan ya ce kiran Obadare ya kasance rashin gaskiya, tsattsauran ra’ayi da wata dabi’ar mulkin mallaka, abin da ya saba tsarin dimokuradiyya.
Ya kara da cewa wasu masu adawa da Shari’a suna neman amfani da Amurka wajen rusa ta ta bayan fage.
Akintola ya jaddada cewa Shari’a hanya ce ta rayuwar Musulmi, kuma tana da cikakken goyon bayan doka, ba za a iya rabata da Musulunci ko kadan ba.
Ya ce duk wanda ya nemi hakan, tamkar yana yunkurin kawar da Musulunci gaba daya ne, don haka ya gargadi ka da a kusanci wannan layin.
'Abin da taba shari'a zai jawo'
Ya nuna cewa tabo Shari’a zai hana gwamnati samun goyon bayan Musulmi masu sassaucin ra’ayi, wadanda ke mara mata baya a yaki da ta’addanci.
Akintola ya tambayi Amurka ko tana yaki da ta’addanci ne ko Musulunci, yana cewa wannan tambaya mai muhimmanci ce ga kasar da ke cewa tana kare Kiristoci.
Ya ce Musulman Najeriya za su ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu muddin an kiyaye haka, amma za su ja daga idan gwamnati ta nemi rusa Shari’a.
Shettima: MURIC ta caccaki Fasto a Najeriya
Mun ba ku labarin cewa kungiyar nan ta MURIC mai kare hakkin Musulmi ta ba fitaccen Fasto a Arewacin Najeriya, Rabaran Ezekiel Dachomo shawara.
MURIC ta caccaki Rabaran Dachomo kan ikirarin cewa gwamnatin Bola Tinubu ta Musulmi da Musulmi ta haifar da “kisan gilla ga Kiristoci”.
Kungiyar ta kuma yi zargin cewa ikirarin “kisan Kiristoci” wata dabara ce don neman kujerar siyasa ba ainihin kare mabiya addinin ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

