Gwamnatin Abba Ta Shaidawa Tinubu Lamarin Rashin Tsaro a Jihar Kano
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa rahoton halin tsaro da jiharsa ke ciki ya karasa kunnen Shugaban Kasa, Bola Tinubu
- Ya bayyana cewa tuni Shugaban ya bayar da umarnin kawo wa Kano agaji ta hanyar aiko tawagar tsaro ta musamman zuwa sassan jiha
- Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa yana aiki tukuru domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a, tare da daukan matakai na musamman
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara tsaurara dabarun tsaro a yankunan da ake kallon suna da rauni, domin dakile barna da dawo da zaman lafiya.
Da yake bayani, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya yi wa Shugaban Kasa jawabi kan yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa musamman a kan iyakar Kano da Katsina.

Kara karanta wannan
Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa Shugaban Kasa ya tabbatar wa da gwamantin Kano cewa za a dauki matakan da suka dace wajen kare rayukan jama'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya shaidawa Tinubu matsalar tsaro
Rahoton ya kara da cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarni a kan a aiko tawagar tsaro domin a ba wa Kanawa kariya.
A cewarsa:
“Na yi wa Shugaba Bola Tinubu cikakken bayani kan yadda barazanar ta tsananta. Ya fahimci girman lamarin, ya kuma bayar da umarnin tura tawagar tsaro ta musamman zuwa Kano.”

Source: Facebook
Ya bayyana cewa ana kammala shirye-shirye na ƙara motoci, ƙarfafa kayan aiki, da samar da ƙarin tallafin aiki domin rundunonin tsaro su samu damar fatattakar ‘yan bindiga.
Gwamnan ya nanata cewa gwamnatinsa ba za ta bar ko wane yanki ba tare da kariya daga ayyukan bata-garin mutane ba.
Gwamnan Kano ya gana da jami'an tsaro
Yayin ziyarar tantance matakan tsaro a sansanonin jami'an tsaro da ke Tsanyawa da Shanono, Gwamna Abba ya sake jaddada shirin saye ƙarin kayan aiki domin ƙarfafa sa ido da gaggawar kai dauki.
Wannan ziyara ta biyo bayan watanni da dama da rikice-rikice ke ta ƙaruwa a yankin, tare da sace mutane, kashe-kashe, da tsoratar da al’umma.
Ya roki jama’a su rika ba jami’an tsaro sahihin bayanan leƙen asiri, yana mai cewa hakan shi ne mafi dacewa wajen gano barazana da hana hare-hare tun kafin su faru.
'Yan ta'adda sun kai hari a Kano
A baya, mun wallafa cewa a karshen mako da ya gabata, ‘yan bindiga dauke da makamai sun sake kai hari a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Shanono a Kano, lamarin da ya kara dagula hankulan jama'a.
Maharan sun kutsa kauyukan Unguwar Tsamiya da ke Faruruwa da Dabawa, inda suka yi harbi a iska, suka sace mutane da dama, tare da raunata wasu a harin da ya zo wa jama'a a ba zata.
Wata majiya daga karamar hukumar Shanono ta tabbatar da faruwar lamarin — inda ake ci gaba da tattara bayanai. Amma a halin yanzu, an ce mutane kusan 25 aka sace, yayin da wasu biyu suka samu rauni.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

