Kasa Ta Rikice: ’Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Kusa a APC
- Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da jigon jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya yayin da ake kokarin kakkabe su
- Maharan sun sace dan siyasar a lokacin da yake barin ofishinsa da misalin ƙarfe 7:00 na yamma a cikin makon nan
- Shaidu sun ce maharan uku dauke da bindigogi sun tilasta masa shiga mota mai launin shudi, tare da kwace wayarsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Wani jigo a jam’iyyar APC ya shiga hannun yan bindiga bayan sun yi garkua da shi a jihar Oyo.
Maharan sun dauke dan siyasar ne a karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Yamma ta jihar Oyo da yammaci.

Source: Facebook
Rahoton Leadership ya ce an dauke Hon. Wale Oriade da yammacin ranar Laraba 3 ga watan Disambar 2025.
Yadda 'yan bindiga suka sace dan APC
Majiyoyi sun bayyana cewa an yi garkuwa da Oriade ne yayin da yake barin ofishinsa da yake a yankin Akala a birnin Ibadan, da misalin ƙarfe 7:00 na yamma.
A cewar wani mai amfani da Instagram, Taoreed Sanusi, wanda ya bada labarin, ya ce wasu mahara uku dauke da bindigogi ne suka tare shi, suka tilasta masa shiga wata mota mai launin shudi kafin su tafi da shi.
An ce motar kirar Micra, wacce ake yawan amfani da ita wajen sufuri a Ibadan, ta zama ana yawan amfani da ita wurin ayyukan ta’addanci a birnin.
Sanusi ya ce:
“Maharan sun tsere zuwa wani bangare da ba a sani ba, kuma sun kwace wayarsa. Lafiyarsa ita ce babban damuwarmu yanzu.”

Source: Original
Tsohon sanata ya nuna damuwa kan lamarin
A martaninsa, tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattijai kuma dan takarar gwamnan Oyo a APC a 2023, Sanata Teslim Folarin, ya nuna bakin cikinsa game da haka.
Ya ce:
“Na shiga damuwa matuƙa da jin an yi garkuwa da Hon. Wale Oriade. Wannan abin ba zai karbu ba, kuma yana tunasar da mu tsananin matsalar tsaro da ke addabar ƙasarmu.”
Sanatan ya yi kira ga hukumomin tsaro su dauki mataki cikin hanzari tare da amfani da dukkan kayan aiki domin ganin an ceto shi cikin koshin lafiya.
Haka kuma, Folarin ya mika sakon ta'aziyyarsa da addu’oinsa ga iyalin wanda aka sace, tare da kira da a kwantar da hankalin magoya bayan jam’iyya da mazauna yankin yayin da hukumomin tsaro ke tsananta bincike.
Ya ce:
“Ba za mu bari jihar Oyo ta fada hannun miyagu ba. Dole mu ƙarfafa tsaronmu, mu inganta raba bayanan sirri, mu kare kowane ɗan ƙasa. Allah ya kiyaye Hon. Oriade, ya dawo mana da shi lafiya.”
'Yan bindiga sun sace iyalin shugaban APC
An ji cewa 'yan bindiga sun kai hari gidan shugaban jam'iyyar APC, Alhaji Muhammad Swasun, inda suka yi awon gaba da matarsa da ’yarsa.
An ce miyagun sun yi barin wuta a cikin garin Patigi da ke jihar Kwara, lamarin da ya tsoratar jama'a, yayin da suka tsere da matan biyu.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya yi bayani game da harin da 'yan bindigar suka kai gidan shugaban APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


