An Kakaba Dokar Hana Fita a Kogi bayan Haramta Dukkan Bukukuwan Addini
- Shugaban Karamar Hukumar a Kogi ya kawo hanyoyin dakile matsalolin tsaro da ke damun al'ummarsa
- Hon. Edibo Peter Mark na karamar hukumar Omala ya kafa dokar hana fita daga ƙarfe 7:00 na dare zuwa 6:00 na safe
- Wannan mataki na da nasaba da matsalolin tsaro da ake fuskanta a yankin musamman sace-sacen al'umma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Omala, Kogi - Shugaban Karamar Hukumar a jihar Kogi ya damu kwarai game da matsalolin rashin tsaro a yankinsa.
Shugaban da ke jagorantar karamar hukumar Omala ta jihar Kogi, Edibo Peter Mark, ya sanar da kafa dokar hana fita.

Source: Facebook
Kogi: An sanya dokar hana fita
Rahoton Tribune ya ce Mark ya kafa dokar ce daga yammaci zuwa wayewar gari sakamakon ƙaruwa da matsalolin tsaro a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan dokar hana fita za ta fara ne daga ƙarfe 7:00 na dare zuwa 6:00 na safe, tun daga ranar 2 ga Disamba, kuma za ta ci gaba har sai wani sabon umarni ya fito.
An kuma bayyana cewa za a gudanar da tsaron sintiri na sa’o’i 24 a dukkan al’ummomin da ke ƙaramar hukumar domin tabbatar da kariyar rayuka da dukiyoyin jama’a.
A cikin wata sanarwa, shugaban karamar hukumar ya ce matakin ya zama wajibi ne domin ɗaukar gaggawar da za ta kare jama’a daga barazanar tsaro da ke ta ƙaruwa a yankin.
Ya kara da cewa, don ƙara tsaurara tsaro, ya umurci jami’an tsaro su ƙara bincike a dukkan hanyoyin shiga yankin, tare da tsauraran binciken ababan hawa tare da cikakken tura Rundunar Hadin Gwiwa (Joint Task Force).
Hukumar ta kuma sanya doka kan tarukan addini kamar Mauludi da sauran bukuwan Kirista, inda ta ce:
“Dukkan tarukan jama’a, ciki har da Moulud, bautar dare na Kiristoci da sauran makamantansu, an dakatar da su har sai wani lokaci.”

Source: Original
Dokokin da aka sanya wa masu ibada
Haka kuma, an haramta yin wasa da wuta (fireworks) na bukukuwa, yayin da coci da masallatai aka umarce su da su takaita lokacin ibada, cewar Daily Post.
A cewarsa: “
Ayyukan bauta a coci ranar Lahadi da salla a masallatai su kasance gajeru, kuma a rufe su da wuri.”
Shugaban karamar hukumar ya roƙi mazauna yankin su yi biyayya ga doka tare da aiki da jami’an tsaro domin a dawo da zaman lafiya gaba ɗaya.
Ya ce haɗin kan jama’a yana da matuƙar muhimmanci wajen taka rawar gani a kokarin dawo da kwanciyar hankali a yankin.
Gwamnatin Kogi ta sha alwashi kan yan bindiga
A wani labarin, gwamnatin jihar Kogi ta nuna damuwa bayan 'yan bindiga sun kutsa cikin wani coci a jihar Kogi inda suka yi awon gaba da fasto, matarsa da masu ibada.
Gwamnatin ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ba da tabbacin cewa tuni hukumomin tsaro suke kokarin ceto mutanen.
Hakazalika ta bukaci cibiyoyin ibada da ke wajen gari a yankunan da ke fama da rashin tsaro da su sake duba yadda suke gudanar da harkokinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


