Hotunan yadda aka gudanar da shagalin bikin Maulidi a wasu jihohin Najeriya
- An gudanar da bikin Maulidi a wasu jihohin Najeriya a yau Alhamis, 29 ga watan Oktoba
- Al'umman Musulmi a duniya kan raya kowace ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal ta kalandar Musulunci domin murnar zagayowar haihuwar Annabi Muhammad
- Mun kawo maku yadda shagalin ya gudana a wasu sassa na kasar
A yau Alhamis, 29 ga watan Oktoba ne al’ummar Musulmi a duniya suka gudanar da bikin Maulidi domin murnar zagayowar ranar haihuwar manzon Allah, Annabi Muhammadu (SAW).
Harma gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da yau Alhamis a matsayin hutu domin raya wannan rana.
Kamar yadda tahiri ya nuna, an haifi manzo tsira a ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal a kalandar Musulunci.
KU KARANTA KUMA: Bukin Maulud: Sauƙon Gwamna Obaseki ga Musulman Edo
Bikin maulidin bana ya zo da sauyi domin an gudanar da shagalin ne daga safe zuwa yamma sabanin yadda aka saba a yi cikin dare saboda dokar takaita lokutan zirga-zirga.
A wasu jihohin kasar, an dai sanya dokar takaita zirga-zirga saboda rikicin da aka yi sakamakon zanga-zangar EndSARS.
Ga hotunan yadda bikin Maulidin ya gudana a jihohin Kaduna da Gombe kamar yadda jaridar Aminiya ta wallafa:
KU KARANTA KUMA: Bukin Maulud: Muhimman abubuwa 5 da Buhari ya faɗa wa yan Nigeria

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
A gefe guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki 'yan Najeriya da su yi koyi da kyawawan halayen annabi Muhammadu (SAW) a sakon bikin Maulidi.
Su nuna kauna da fahimta ga al'umma, da kuma bayyanar da kyawawan halayensa na hakuri, gaskiya, rikon amana da mutunci ga kowa, Premium Times.
A wani sako da shugaban kasa ya tura wa musulmai a kan maulidin fiyayyen halitta, wacce ta zama ranar hutu a Najeriya, shugaban kasa ya roki 'yan Najeriya musamman matasa da su bar duk wani mummunan kudiri a kan zanga-zangar da ke gudana.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng