Tinubu Ya Tura Sako na Musamman ga Majalisa bayan Tabbatar da Nadin Ministan Tsaro

Tinubu Ya Tura Sako na Musamman ga Majalisa bayan Tabbatar da Nadin Ministan Tsaro

  • Bola Ahmed Tinubu ya fito ya yabi Majalisar Dattawa bisa hanzarta amincewa da nadin sabon Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa
  • A ranar Talata da ta gabata Tinubu ya tura sunan Janar Musa kuma Majalisar Dattawa ta tantance shi tare da tabbatar da nadinsa ranar Laraba
  • Shugaban kasa ya bayyana tsohon sojan a matsayin mutumin kirki kuma nagari, inda ya ce nadinsa na da matukar muhimmanci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aike da sakon yabo ga Majalisar Dattawa bayan ta kammala aikinta kan sabon Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa.

A jiya Laraba, 3 ga watan Disamba, 2025 Majalisar Dattawa ta tantance Janar Musa (mai ritaya) bayan kwashe sa'o'i masu yawa yana shan tambayoyi daga sanatoci.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zauren Majalisar Tarayya Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta ce hakan ya biyo bayan nadin da Tinubu ya masa tare da tura sunansa ga majaliaar dattawa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro, Janar Musa ya ware gwamnoni 6 da suka yi fice a kokarin samar da tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin Janar Musa a Majalisar Dattawa

Yayin tantance shi, Janar CG Musa, wanda bai jima da sauka daga kujerar babban hafsan tsaron kasar nan ba, ya sha alwashin cewa ba zai ba 'yan Najeriya kunya ba.

Sabon ministan ya bayyana cewa ya fahimci kyakkyawan zato da tsammanin da 'yan Najeriya ke masa, kuma zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya shafe masu hawaye.

Musa wanda ya shekara kusan shekaru 40 a gidan soja ya shafe awanni biyar ana yi masa tambayoyi.

Bola Tinubu ya yabawa Majalisar Dattawa

Da yake nuna farin cikinsa kan tabbatar da nadin Janar Musa da Majalisar Dattawa ta yi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gode wa sanatocin gaba daya.

Bola Tinubu ya bayyana godiyarsa ga Majalisar Dattawa ne saboda gudunmawar da ta bayar wajen hanzarta tabbatar da Janar Christopher Musa (mai ritaya) a matsayin sabon Ministan Tsaro.

A rubutun da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, Shugaban ya ce:

Kara karanta wannan

A karshe, majalisa ta amince da nadin Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaro

"Kwanaki biyu da suka wuce, na aika sunan Janar Christopher G. Musa, tsohon Babban Hafsan Tsaronmu kuma mutumin kirki, ga Majalisar Dattawan Najeriya don a tabbatar da shi a matsayin Ministan Tsaro."
"Ina yabawa Majalisar Dattawa bisa kokarin da ta yi wajen tabbatar da madin Janar Musa ba tare da daukar dogon lokaci ba a jiya.
"Wannan nadin nasa ya zo ne a wani mawuyacin lokaci a rayuwarmu a matsayin Kasa.
Janar Christopher Musa.
Ministan Tsaron Najeriya, Janar Chirstopher Musa Hoto: NGRSenate
Source: Twitter

Tinubu ya bayyana tsohon hafsun a matsayin “mutum nagari” kuma ya ce nadin nasa na da matuƙar muhimmanci ga makomar tsaron ƙasar nan a wannan lokaci mai cike da ƙalubale.

Ya ƙare da addu’ar cewa:

“Allah ya albarkaci Tarayyar Najeriya.”

Abin da 'yan Najeriya ke fata daga Janar Musa

A wani rahoton, kun ji cewa wani sanannen lauya mazaunin Abuja, Pelumi Olajengbesi ya yi tsokaci kan nadin Janar Christopher Musa a matsayin Ministan Tsaron Najeriya.

Ya ce jama'a na fatan sabon ministan zai yi amfani da kwarewarsa wajen kawo canje-canje a dabarun yaki da ta'addanci, yana mai kira ga Janar Musa da kada ya ba mutane kunya.

Kara karanta wannan

'Ba mu yarda ba,' Majalisa ta rikice yayin da ake tantance sabon ministan tsaro

Olajengbesi ya bayyana Janar Musa a matsayin daya daga cikin fitattun hafsoshin sojin kasar nan da babu wani tabo mara kyau a jikinsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262