Jirgin Fadar Shugaban Kasa Ya Yi Kwantai bayan Dogon Lokaci a Kasuwa

Jirgin Fadar Shugaban Kasa Ya Yi Kwantai bayan Dogon Lokaci a Kasuwa

  • Jirgin fadar shugaban kasa da Najeriya ta saka a kasuwa ya shafe kusan watanni biyar ba tare da an iya samun mai saye ba
  • Kamfanin JetHQ ya cire jirgin daga jerin irgaen da ke kasuwa, yana mai cewa a tuntubi gwamnatin Najeriya domin karin bayani
  • Jirgin Boeing 737 BBJ da aka saya a 2005 darajarsa yanzu na kusan Dala miliyan 56, wanda ya haura N82bn a kudin Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Jirgin Fadar Shugaban Kasa da Gwamnatin Najeriya ta saka a kasuwa ya yi kwantai duk da cewa ya shafe kusan watanni biyar yana yawo a shafukan kasuwancin jiragen sama na duniya.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnati ta yi bayani kan dokar hana acaba, an yi sassauci a wasu yankuna

Saboda wannan cikas, kamfanin JetHQ — wanda ke da alhakin tallata jirgin — ya cire duk wasu bayanansa daga dandalin sayar da shi.

Jirgin Fadar Shugaban Kasa ya yi kwantai
Daya daga cikin jiragen fadar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: ASO VILLA
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa an tabbatar da wannan ne ta hanyar imel da Manajan Binciken Kasuwa na JetHQ, Laurie Barringer, ya aika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin saman Najeriya ya yi kwantai

Aminiya ta wallafa cewa Laurie Barringer ya tabbatar da cewa jirgin ya fita daga jerin kayayyakin da kamfanin ke sayarwa saboda babi wanda ya saye shi.

Barringer ya shawarci duk masu neman karin bayani su tuntubi gwamnatin Najeriya kai tsaye, yana mai cewa:

“Ba mu da jirgin Boeing a halin yanzu kan jerinmu. Gwamnatin Najeriya ce za ta ba da karin haske.”

Sai dai duk da cewa Hadimin Mai Ba da Shawara kan Tsaron Ƙasa, Ismail Garba, ya ce zai yi bayani kan lamarin, har yanzu ba a samu karin bayani ba.

Kara karanta wannan

Tsohon hafsan tsaro, Janar Irabor ya fadi 'yan siyasa masu rura wutar matsalar tsaro

Yadda aka sa jirgin Najeriya a kasuwa

Daga baya, Barringer ya kara fayyace cewa kamfanin ba shi da ikon fitar da wasu bayanai saboda dokokin sirri da ke kare mallakar mai jirgin, yana mai cewa a tuntubi gwamnatin Najeriya.

Kafin a cire shi daga kasuwa, rahotanni sun nuna cewa an yi wa jirgin sababbin gyare-gyare a watan Yuli 2024, ciki har da sabunta kujerun ajin farko da wasu kananan gyare-gyare na cikin jirgi.

Gwamnati ta ki karin bayani a kan jirginta da ya yi kwantai
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

An fara mallakar wannan jirgin ne a 2005 lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, inda aka saya shi kan Dala miliyan 43, kuma tun daga lokacin yake cikin jerin jiragen Fadar Shugaban Ƙasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da babban hafsan tsaron Najeriya da ya kora daga aiki

A cikin Yuli 2025, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sanar da cewa za ta sayar da jirgin domin rage kashe kuɗIn gudanarwa da kuma daidaita adadin jiragen da ake amfani da su.

Wannan mataki ya zo ne yayin da ’yan ƙasa ke ƙara saka idanu kan yadda kudIn jama’a ke tafiya, musamman a wannan lokaci da tattalin arzikin ƙasa ke fuskantar ƙalubale.

Fadar shugaban kasa ta yi gargadi

A baya, mun wallafa cewa Fadar shugaban kasa ta bayyana damuwa kan yadda rahotanni marasa tushe na zargin yunkurin juyin mulki ke yawo tana mai cewa irin wadannan jita-jita na iya jawo mummunar illa ga kasa.

Mai magana da yawun Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka a karin bayani game da halin da ake ciki kan rahoton yunkurin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce a halin da ake ciki, gwamnati na ƙoƙarin jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje, don haka duk jita-jitar da ke nuna rashin kwanciyar hankali tana iya bata sunan ƙasa.

Kara karanta wannan

Abubakar Malami ya yi bayani game da 'kudin Abacha ' da EFCC ke zargin ya yi wasosonsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng